Muna so shugaba Tinubu ya dawo da tallafin man fetur – Ƙungiyar ‘yan Arewa

0
90

Daga Ibraheem El-Tafseer

Wata Ƙungiyar arewa da ke sanya idanu kan harkokin tattalin arziƙi (Arewa Economic Forum), ta yi tsokaci kan halin da tattlin arziƙin ƙasar ke ciki, inda ta yi ƙira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sake nazari kan manufar cire tallafin man fetur da kuma dakatar da raba kuɗaɗen da ake yi wa gwamnonin jihohi.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Shehu Ibrahim Ɗandakata, wanda ya yi jawabi ga manema labarai a ranar Alhamis a Abuja, ya ce rashin bin diddigi da kuma rashin mai da hankali kan muhimman abubuwa da gwamnoni ke yi shi ya sa talauci da yunwa suka yi ƙamari a ƙasar.

A madadin sake dawo da biyan tallafin man fetur, ƙungiyar ta yi ƙira ga shugaban ƙasa da ya nemo hanyoyn da za a tabbatar da cewa gwamnonin jihohi sun yi amfani da rarar kuɗaɗen da ake kasafta musu ta hanyoyin da suka dace domin kuɗaɗen su yi tasiri kan al’umma.

KU KUMA KARANTA: DSS ta gargaɗi ƙungiyar ƙwadago ta Najeriya a kan shirin zanga-zangar ‘tsadar rayuwa’

Ɗandakata ya kuma buƙaci gwamnatin tarayya da ta duba halin da darajar kuɗin ƙasar ke ciki, ta kuma binciki dalilin da ya sa farashin dala ke tashi bayan duk wani taron kwamitin raba arziƙin ƙasa (FAAC).

Leave a Reply