Ƙasashen Waje
Ministocin Tsaron Turkiyya da Djibouti sun sa hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta soji
![](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/02/Screenshot_20240220-073432_1.jpg)
Manyan hafsoshin tsaron Turkiyya da na ƙasar Djibouti ta gabashin Afirka sun sa hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyi da ƙa’idoji a birnin Ankara, waɗanda suka haɗa da yarjejeniyar hadin gwiwa ta horar da sojoji, da yarjejeniyar hadin gwiwar hada-hadar kuɗi ta soji, da kuma yarjejeniyar aiwatar da tallafin kuɗi.
Ma’aikatar tsaron kasar ta bayyana cewa, a hukumance Minista Yasar Guler ya yi maraba da Ministan Tsaron Djibouti Hassan Omar Mohamed a ranar Litinin, wanda ya isa birnin Ankara a matsayin baƙo, tare da bikin soji. Bayan kammala bikin, ministocin biyu sun ci gaba da taron ƙasashen biyu.
Ma’aikatar ta ce a ƙarƙashin jagorancin hafsoshin tsaron biyu an gudanar da wani taro na matakin tawaga.
KU KUMA KARANTA: Turkiyya na fatan bunƙasa kasuwanci da Saudiyya zuwa dala biliyan 30
Ma’aikatar ta ce, a taron wanda ya samu halartar kwamandan rundunar sojin ƙasa ta Turkiyya Janar Selcuk Bayraktaroglu, hafsoshin tsaron sun rattaba hannu kan yarjeniyoyi uku.
Ƙasar Djibouti mai yawan al’umma ƙasa da miliyan guda, tana wuni muhimmin yanki a Gaɓar Tekun Aden a matsayin hanyar wucewa ta Bahar Maliya.
Ƙasashen Waje
Masu zanga-zanga sun hana jirage fiye da 100 tashi
![Masu zanga-zanga sun hana jirage fiye da 100 tashi](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/images-12.jpeg)
Masu zanga-zanga sun hana jirage fiye da 100 tashi
Masu zanga-zangar rajin kare muhalli sun hana fiye da jirage 100 tashi a filin jirgin saman birnin Frankfurt da ke zaman mafi yawan hada-hadar jiragen sama a Jamus.
Dubban masu rajin kare muhallin sun tsara gudanar da zanga-zanga a ƙasashen Turai baki ɗaya, domin daƙile zirga-zirgar jiragen sama a daidai lokacin da mutane da dama ke tafiya hutun bazara da nufin nuna illa da barazanar sauyi ko ɗumamar yanayi.
Rahotanni daga filin jiragen saman na Frankfurt sun nuna cewa masu zanga-zangar sun karya shingen jami’an tsaro tare da kutsa kansu kan titunan jiragen saman.
KU KUMA KARANTA: Za mu kare masu zanga-zanga in dai ta lumana ce – IGP
DW ya ruwaito cewa wannan lamari dai ya tilsta ’yan sanda da jami’an kashe gobara da sauran jami’an tsaron filin jiragen saman ɗaukar mataki.
Masu zanga-zangar dai sun tilasta soke tashin kimanin jiragen sama 140, kuma kawo yanzu babu wani ƙarin bayani kan sabon lokacin da aka tsara tashinsu saboda fargabar sake samun kutsen ’yan rajin kare muhallin.
Ƙasashen Waje
Wani jirgin sojin Rasha ya faɗi a kusa da Ukraine
![Wani jirgin sojin Rasha ya faɗi a kusa da Ukraine](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/IMG_20240725_142333.jpg)
Wani jirgin sojin Rasha ya faɗi a kusa da Ukraine
Wani jirgin sojin ƙasar Rasha samfurin Mi-28 ya faɗo a wani yanki da babu kowa a Kudu maso yammacin kasar.
Hatsarin jirgin mai sauƙar ungulu ya yi ajalin ma’aikatan jirgin, kamar yadda wasu kamfanonin dillancin labaran ƙasar Rasha suka sanar a ranar Alhamis.
Kamfanin dillancin labarai na TASS ya ambato wata majiya a ma’aikatar tsaro ta ce “helkiwafta ƙirar Mi-28 ya fado a yankin Kaluga, ma’aikatan jirgin sun mutu.”
“Bayanan farko sun nuna wata matsalar fasaha ce ta haddasa hatsarin jirign,” in ji kamfanin dillancin labarai na Interfax, yana ambato wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Rasha ta fitar.
KU KUMA KARANTA: Hatsarin jirgin sama ya yi sanadiyar mutuwar mutum 18
Hatsarin jirgin sojin ya faru ne ne a wani daji mai tazarar kilomita 150 daga kan iyakar ƙasar Rasha da Ukraine, kamar yadda wani jami’in yankin ya shaida wa TASS.
Haɗarin ya afku ne a wani daji mai nisan kilomita 150 daga kan iyakar ƙasar ta Ukraine.
Ƙasashen Waje
Kusan mutane miliyan 26 a Sudan na fama da matsananciyar yunwa – MƊD
![Kusan mutane miliyan 26 a Sudan na fama da matsananciyar yunwa - MƊD](https://neptuneprimehausa.com/wp-content/uploads/2024/07/20476412_0-0-768-433.jpeg)
Kusan mutane miliyan 26 a Sudan na fama da matsananciyar yunwa – MƊD
Kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya, Stephane Dujarric, ya bayyana damuwa game da taɓarɓarewar yanayi na ƙarancin abinci a Sudan.
“Kusan mutane miliyan 26 da suka haɗa da maza manya, mata da yara ƙanana ne suke fama da bala’in yunwa – misali shi ne, adadin ya kai yawan mutanen Australia baki ɗaya,” in ji Dujarric, kamar yadda ya faɗa wa ‘yan jaridu.
Daga cikin mutane miliyan 26, 750,000 na dab da afkawa cikin bala’in yunwa da rashin abinci, in ji kakakin Majalisar Ɗinkin Duniya (MƊD).
Ya ƙara da cewa “Mutane a Sudan na fuskantar yanayi mafi muni a rayuwarsu”.
Sudan ta faɗa ƙazamin rikici inda rundunar sojin ƙasar ƙarƙashin Janar Abdul Fattah Al Burhan ke arangama da mayakan rundunar kai ɗaukin gaggawa ta RSF da tsohon mataimakin shugaban ƙasar Mohamed Hamdan Fagalo ke jagoranta.
KU KUMA KARANTA: Amurka ta ba da tallafin dala miliyan 203 don ƙarin taimakon jinƙai ga Sudan
Aƙalla mutane 12,260 ne aka kashe sannan sama da 33,000 suka jikkata a rikicin da aka fara a watan Afrilun 2023, kamar yadda alƙaluman MƊD suka bayyana.
Rikicin jinƙai na ci gaba inda kusan mutane miliyan 6.8 suka bar gidajensu tare da neman mafaka a cikin Sudan ko ƙasashe maƙota.
Ba a samu nasarar yarjeniyoyin tsagaita wuta daban-daban da Saudiyya da Amurka suka jagoranta ba da nufin kawo ƙarshen rikicin.
-
Kotu1 year ago
Kotu tayi watsi da ƙarar APC game da zaɓen Abba Gida Gida
-
Labarai10 months ago
Dalilin da ya sa na saka wa matata sasari – Wani magidanci a Potiskum
-
Ƙasashen Waje1 year ago
Ɗaliban Najeriya a Sudan sun nemi a kwaso su daga ƙasar
-
Labarai1 year ago
‘Yan banga sun kama wani mutum da ke yunƙurin sace yarinya a Kano