Miji ya saki matarsa bayan ta nemo masa kuɗin zuwa Saudiya

1
1233

Wata mata mai shekaru 45, Karima Nuhu, a ranar Talata ta maka mijinta, Musa Falalu, a gaban wata kotun shari’a da ke zamanta a Rigasa, Kaduna, bisa zargin ƙin kai ta ƙasar Saudiyya.

Mai shigar da ƙarar da ke zaune a unguwar Rigasa a Kaduna ta shaida wa kotun cewa ta yi aure da Falalu tsawon shekara huɗu inda ya ba ta abinci na tsawon wata biyu kacal, tun da suka yi aure.

KU KUMA KARANTA: Fitaccen ɗan fim, Adam A. Zango ya saki matarsa Safiya

“Ya shaida min cewa ya rasa aikinsa na direba amma ya samu wani a Saudiyya, inda ya buƙace ni da in yi hakuri yayin da ya yi alƙawarin zai ɗauke ni mu tafi can.

“Ya zuwa yanzu, duk shekarun nan Ni ke ciyar da kaina. Har ma na aro masa kuɗi domin ya samu kuɗin tafiyar dani, amma bayan samun abin da yake so, sai ya sake ni,” inji ta.

1 COMMENT

Leave a Reply