Daga Ibraheem El-Tafseer
Yadda wata matashiya ‘yan asalin Najeriya ke tuna irin cin zarafi da wahalhalun da ta fuskanta a kan hanyarta ta tafiya ci-rani nahiyar Turai kenan.
Mun sakaya sunan wannan matashiya muka sa mata suna Ada saboda wannan labarin.
Ta faɗa tarkon masu safarar mutane ne a 2016, lokacin tana ‘yar shekara 20.
Aikin gyaran gashi take yi a Jihar Delta, kuma mutumin da ya yi mata romon-baka ya nuna mata cewa yana da ‘yar uwa da take gyaran gashi a Turai, kuma Turawan suna son yadda ‘yan Najeriya suke gyaran gashi sosai.
KU KUMA KARANTA: An kori malamar jinyar da ta yi lalata da marar lafiya
Wannan shi ne asalin abin da ya sanya Ada barin gida, da zummar za ta je Turai kai-tsaye domin ci gaba da sana’ar da take yi a Najeriya.
Amma ta kwana da sanin cewa hanyar ƙasa za su bi su tafi ba jirgi za su hau ba, domin kuwa ko fasfo ba ta da shi.
Cikin motar awaki aka zuba mu daga Nijar.
“Tafiyarmu ta Nijar ta fara — daga Nijar ne mun bi ruwa mun bi rana, mun shiga sahara kuma mun kusa wata guda cikinta.
“Wani buzu ne ya kwashe mu a motarsa, muka ɗauki hanya ban da tsayin kwana da tuni na mutu a wannan saharar, motar da muka shiga muna da yawa mun kai 20 maza da mata a kwance a but ɗin motar.”
“A kwance muke kafada-da-kafada, wasu mutane da ke cikin saharan sun tsayar da mu, suka tambayi direban su waye a cikin motar, direban ya ce tinkiyoyi ne a ciki, a raina na ce ‘ohh wai ni ce tinkiya.’”
“Da yake motar a lulluɓe take da tamfol, sai suka ce a cire shi su gani, kamar shi buzun da ya ɗauko mu yana da asiri a jikin zobensa, yana mirzá zoben sai ya buɗe ga mu dai a ciki amma tinkiyoyi suke gani,” in ji Ada .
Ada ta ce a ƙarshe sun samu shiga Aljeriya zuwa wani gari da ake kira Oran.
Masu HIV na cikin waɗanda suka rika yin lalata da mu.
Ba Ada ce kaɗai ta fuskanci irin wannan tashin hankalin ba, akwai ɗaruruwan matasa da ke irin wannan tafiya daga nahiyar Afrika, babu wanda ke tsira daga maza har mata.
A Aljeriya akwai wata tashar da ake jibge ‘yan ci-ranin da suke bin hanya domin shiga Morocco, za su jira har sai an saci numfashin jami’an lura da shige da fice sai a tsallaka da su Rabat.
An ajiye su Ada a wannan wuri kimanin watanni biyu, kuma a cikin wasu ɗakunan tamfol suke kwana, babu dare babu rana maza ne kawai ke tsallakowa suna zaɓar matan da za su je su kwanta da su.
“Ni dai ba a min wannan cin zarafin ba saboda mu ‘yan matan Oga ne, ya faɗa tun kafin mu ƙaraso cewa ka da wanda ya kusance mu, mun huta a wurin, abin da ba a yi a wajen kamar sanya gajeren wando da ƙaramar riga mu duk sai da muka yi, babu wanda ke taɓa mu.”
“Cikin waɗanda suka riƙa neman matan da ke wurin akwai waɗanda ba su da lafiya, ana zargin HIV ce da su, a cikinsu akwai waɗanda muna wannan wurin suka mutu, ba ruwansu da amfani da kororon roba, in ma kin yi ciki babu ruwan kowa,” in ji Ada.
“Yadda na fara karuwanci a Morocco”
“Da aka kai ni Morocco sai na nemi na kama gabana a Casablanca, sai aka ce ai ba ni da ‘yancin tafiya saboda ana bi na bashi matar da ta biya kuɗi aka yi jigila da ni daga Najeriya zuwa.”
“Dirham 30,000 kwatankwacin yuro €4,000 ake nema daga hannuna, sune kuɗin jigilar, ba ni da yadda zan yi na sami waɗannan kuɗin, don haka ba ni da wani zaɓi sai dai na yi karuwanci”, in ji Ada.
Farashi aka yi wa matan gidan na bai ɗaya kuma ita mai lura da su tana rubuta yawan maza da kuɗin da yarinya ke samu, idan takai iyakar abin da za ta biya shikenan sai ta sallame ta.
Sai da Ada ta yi zaman gidan na kusan shekara biyu da rabi kan ta iya biyan kuɗin da ake binta.
Ta ce idan za a kwana Dirhami 300 ake biya idan kuma kwanciyar ta ɗan lokaci ce Dirhami 200 ne, kuma ko kwana mutum ya biya, sai kwanta da ita ne sau biyu kacal a daren.
Mafiya yawan matafiyan kan tsintar kansu a wasu sabbin wurare da ba su sani ba, ba kuma su yi mafarkin za su taɓa zuwa ba, wani lokaci ba sa jin yaren ƙasashen da suke ratsawa ta cikinsu, amma fatan samun rayuwa mai kyau da gujewa wahalhalun da suke iƙirarin suna sha a ƙasashen ne ke ƙara ingiza su.
Lokacin da suke isa Moroco sukan ji cewa sun ci kashi 80 na wahalar tafiyar ciranin tasu, to amma tsallaka Morocco zuwa Turan a cewarsu, ya fi wuya in aka kwatanta da wahalhalun da suka baro a baya.
Abin da ya sa ‘yan ci-rani suka fi son shiga Morocco shi ne, ƙasar ta haɗa iyaka da Sifaniya, ta wani gefen tekun za ka iya samun damar shiga Gibrelta daga ƙasar. Akwai iyakoki masu dama da akan bi amma idan mutum ya je garin Tanja shi ne zai ga cincirindon ‘yan ci-ranin.
Hukuma da ke lura da ‘yan cirani ta duniya UNHR ta ce yana da wuya a iya sanin adadin ‘yan ciranin da ake cin zarafi a lokacin da suke ƙoƙarin tsallakawa Turai, saboda dama ba sa faɗa, kuma tun da tafiyar ba ta kaida ba ce ba su da wanda za su kai wa ƙara.
Yanzu dai Ada ba ta iya kai wa inda take so ta je ba, kuma a inda ta maƙale ba ta samun abin da za ta koma gida da shi ta nuna a matsayin ribar tafiyarta.
Sannan gudun jin kunya ka iya sa ta ci gaba da zama a nan, a gefe guda kuma cin zarafin da aka yi mata abu ne da ba zai taɓa gushewa ba a cikin tunaninta.