Mawadata Su Taimaka Wa Al’ummarsu – Sardaunan Nagarta

0
418

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN yi kira ga mawadata da Allah ya ba hannu da shuni da su taimakawa mabukata da ke cikin al’umma kamar yadda addinin musulunci ya bayar da umarnin a aikata musamman a wannan wata na Azumi mai alfarma.

Shugaban al’umma Mu’azu Mohammad Abubakar majidadin Gundumar Afaka kuma Sardaunan Nagarta ne ya yi wannan kiran lokacin da ya tattauna da manema labarai jin kadan bayan Rantsar da shugabannin kungiyar da za su jagoranci kungiyar Kansiloli ta kasa reshen Jihar Kaduna karkashin jagorancin Honarabul Auwalu Sani kansilan mazabar Afaka.

Mu’azu Mohammad Abubakar, ya ci gaba da bayanin cewa hakika taimakawa jama’a na da kyau musamman a wannan watan mai alfarma da ke da dimbin albarka da ake ninkawa jama’a lada ninkin ba ninki don haka duk wanda Allah ya ba abin hannu ko wata wadata ya na da kyau ya duba masu bukata a cikin al’umma ya taimaka masu.

“Ga wadanda kuma ba su da wadata muna kira a gare su da kada su matsawa kansu har mutum ya kai kansa ga halaka, saboda haka hakuri shi ne magani a cikin rayuwar duniya”.

Majidadin Afaka, ya kuma ankarar da jama’a cewa ya na da kyau kowa ya tsaya a inda Allah ya ajiye shi, kuma wanda Allah ya ba dukiya ya sani cewa ba shi kadai aka ba dukiyar ba don haka sai ya raba tare da jama’a baki daya.

Sardaunan Nagarta, Mu’azu Muhammad Abubakar ya tabbatar wa da jama’a cewa “dole ne ayi zabe sai dai idan akwai wani kwakkwaran dalilin da kowa zai iya amincewa da shi tukuna sannan wata magana ta taso, a misali kamar batun matsalar tsaro idan ka san akwai inda zaka je zabe ka samu matsalar lafiyar ka ai ba wani dalilin yin hakan , amma ba abin da zai hana mutum yin zabe domin hakkin mutum ne wanda za a iya yin amfani da kuri’a a cire duk abin da ba a so a koda yaushe kuma a tabbatar da dai- daito a dukkan lamuran kasa baki daya”, Inji majidadin Gundumar Afaka kuma Sardaunan Nagarta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here