Masu kutse sun kai kai hari kan rubun bayanan hukumar zaɓe

0
437

Shugaban Hukumar Zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, ya ce an yi yunƙurin yin kutse a cikin na’urar tattara bayanai na hukumar gabanin babban zaben 2023.

Yakubu ya yi wannan jawabi ne a ranar Alhamis ɗin da ta gabata yayin taron ƙungiyar masu aiko da rahotanni ta ƙasa (NAJUC) a Abuja mai taken, ‘Zaɓen 2023; Shari’a da ɗorewa dimokuraɗiyyar Najeriya.

Shugaban hukumar ta INEC wanda ya samu wakilcin mataimakin daraktan na bangaren fasahar sadarwa ICT, Dr Lawrence Bayode, ya ce hare-haren sun fito ne daga sassa daban-daban na duniya ba Najeriya kaɗai ba.

“Muna duba tsarin a jiya kuma muna ganin cewa mutane na ƙoƙarin shigowa cikin tsarin daga ƙasar Faransa amma kuma muna ɗaukar mataki.

“mutum baze gina gida ba kuma ya kasa sanya ƙofa, ko taga ba, mun yi iya bakin ƙoƙarin mu don ganin cewa tsarinmu ya bada kariya,” in ji Bayode.

Ya ƙara da cewa an samu na’urar tsarin rijistar masu kada ƙuri’a (BVAS) da hukumar zaɓe ta INEC wanda kuma yana da cikakken tsaro da zai yi wuya a yi kutse cikin su.

Bayode ya sake nanata cewa ba za a yi zaɓe ba tare da katin zabe na dindindin (PVC) da kuma tantancewa kamar yadda sashe na 47 (1) na dokar zabe, 2022 ya tanada sai da waɗannan na’ura.

A jawabin babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a Abubakar Malami (SAN) wanda ya samu wakilcin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Dr Umar Gwandu, ya yaba wa kafafen yaɗa labarai kan rawar da suke takawa wajen ɗorewa dimokuraɗiyyar Najeriya, yayin da ya buƙaci masu kada ƙuri’a da su bijirewa rashawar zaɓe, kada su kuma sayar da ƙuri’unsu.

Leave a Reply