Majalisar dattawa ta tabbatar da Bakari a matsayin jagoran hukumar NFIU

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da naɗin Hafsat Bakari a matsayin darakta a hukumar kula da hada-hadar kuɗi ta Najeriya wato NFIU.

Tabbatar da Malama Hafsat a matsayin darakta biyo bayan nazarin rahoton kwamitin yaƙi da cin hanci da rashawa da ke samun jagorancin Sanata Emmanuel Udende Memga da ke wakiltar mazaɓar Benuwe ta arewa maso gabas a majalisar.

A makon jiya ne shugaba Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Hafsat Bakari a matsayin Darakta kuma jagorar hukumar ta NFIU tare da miƙa wa ga Majalisar Dattawa don tabbatar da ita.

KU KUMA KARANTA:Ɓullar cutar sanƙarau a Yobe, ɗalibai sama da 20 sun mutu

A yayin fitar da sanarwa a kan naɗin Hafsat, mai magana da yawun Shugaban Tinubu, Cif Ajuri Ngelale yace Malama Bakari lauya ce kuma ƙwararriya a fannin binciken harkokin kuɗi, wacce ta shafe shekaru da dama a fannin yaƙi da safarar kuɗaɗen haram, ɗaukan nauyin ta’addanci, da kuma yaƙi da cin hanci da rashawa.

A cewar Ngelale, kafin a naɗin Shugabar Hukumar ta NFIU, ta taɓa zama mataimakiyar darakta a sashin kula da harkokin kuɗi na hukumar, kuma ta kasance Shugabar sashen kula da harkokin yau da kullum a lokuta daban-daban, baya ga shugabantar sashen tsare-tsaren dabaru da jagorantar sakatariyar kwamitin hukumar ta hukumar EFCC mai yaƙi da masu yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa.

Bayan naɗin ta, Shugaban Ƙasa na sa ran cewa, Hafsat Bakari za ta yi amfani da ƙwarewa da gogewarta wajen sauƙe nauyin da ya rataya a wuyanta a wannan muhimmin aiki da aka ba ta, musamman ganin yadda gwamnatin Shugaba Tinubu ke ƙoƙarin yaƙi da masu safarar kuɗaɗen ta haramtacciyar hanya, da sauran ayyuka aikata almundahana da kuɗaɗen al’umma da a halin yanzu ake gani a ɓangaren kasuwannin canjin kuɗaɗen waje na ƙasar nan, in ji Ngelale.

Tun bayan fitar da sanarwar Malama Hafsat ne wasu ‘yan Najeriya ke ta tafka muhawara a kan cewa Allah ya sa kar ta baiwa mutane kunya kamar wasu mata da aka baiwa muƙamin musamman na baya-bayan nan.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *