Maganar Buhari Abin Al’ajabi Ne A Najeriya – Shu’aibu Mikati

0
412

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

MASANI a kan harkar tattalin arziki kuma shahararren dan kasuwa kuma tsohon dan takarar Gwamnan Jihar Kaduna a tarayyar Najeriya Alhaji Shu’aibi Idris Mikati, ya bayyana maganar da shugaba Buhari ya yi da ya ba yan kasar hakuri game da batun matsalar man fetur, man Gas, iskar Gas da sauran albarkatun mai da kuma karancin wutar lantarkin da ke addabar yan kasar a matsayin magana ce ta al’ajabi.

Shu’aibu Idris Mikati, ya bayyana hakan ne a lokacin da yake ganawa da kafar yada labarai ta Muryar Amurka sashen hausa, inda ya ce hakika maganar hakurin da shugaba Muhammadu Buhari ya ba yan Najeriya abu ne na al’ajabi domin kuwa ba a samu wani da ya yi hakan ba.

Sai dai Shu’aibu Mikati, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya hanzarta ganin ya aiwatar da umarnin da ya bayar na a zakulo wadanda suka shigo da gurbataccen man fetur har ya yi sanadiyyar rasa ran wasu mutane.

“Mun ji lokacin da shugaba Buhari ya bayar da wannan umarni na a zakulo wadanda ke da hannu wajen aiwatar da hakan na shigo wa da man da ya yi sanadiyyar matsaloli amma kuma ba mu ga an kama kowa ba har yanzu, don haka muke ganin ya dace shugaban ya kara matsa kaimi sai an zakulo mutanen tare da yi masu hukunci domin ya bayar da umarnin a zakulo su”.

Leave a Reply