Léopold Sédar Senghor, ɗan fursunan da ya zama shugaban ƙasa

1
428

Léopold Sédar Senghor, wadda ake yi wa kallon dattijo a Afirka, masani ne kuma marubucin waƙoƙi. Bayan zama gidan yari lokacin yaƙin duniya, ya kasance shugaban ƙasar Senegal na farko.

An haife shi ne a ranar tara ga watan Oktoba, na shekarar Alif da ɗari tlara da Shida (1906), a yankin kudu maso gabashin birnin Dakar na Senegal. Senghor, shi ne jagoran ƙungiyar fafutikar kare baƙar fata ta Négritude, a shekarar Alif da ɗari tara da talatin (1930).

Ya zama shugaban ƙasar Senegal a cikin watan Satumba Alif da ɗari tara da Sittin (1960), bayan zama ɗan jarida daga cikin ayyukan da ya yi. Ya ci gaba da zama shugaban ƙasa na tsawon shekaru sama da Ashirin.Ya rasu a ranar Ashirin ga watan disambar shekerar dubu biyu da ɗaya (2001), a Faransa ya na da shekaru Casa’in da Biyar.

Léopold Sédar Senghor, mutum ne mai son zaman lafiya da kawaici, sannan ya na da son komai ya tafi daidai a tsarinsa na aiki.Masani ne da ke da ƙaunar harsuna. Shi ne baƙar fata na farko da ya shiga majalisar marubuta ta harshen Faransanci wato a shekara ta Alif da ɗari tara da tamanin da huɗu (1984).

Sannan daɗin-dadawa shi ne shugaban ƙasar Afirka na farko da ya yi murabus a bisa raɗin kansa.Ya shahara wajen tsara magana mai hikima cikin kalamai kaɗan. “Ka fahimta, ba don lallai a fahimce ka ba.”

Daga cikin fitattun kalamansa na hikima, Senghor ke kiran matasan Afirka da su yi ƙoƙarin fahimtar duk wani abu da ke da asali da tarihi gami da al’adu, domin ƙarfafa ilimin zuwa ga wani mataki da ya gaza samuwa a zamanin baya.“Ci gaba mai tafiya da zamani.”

Wannan kalma ta samo tushe da kuma ma’anar muhimmancin buɗa hankali don karɓo baƙon abu mai amfani da kuma miƙa shi ga na gaba.Manufar hakan shi ne, haɗa wasu abubuwan na baƙar fata da waɗanda ke da tsatso da turawa domin samun sabuwar tafiya ta baƙar fata ko “New Negro” kamar yadda ya faɗa.Akwai abubuwa na rashin fahimta da suka shafi rayuwar Senghor.

Tsakanin shekarar Alif da Ɗari Tara da Sittin da Biyu, zuwa alif da ɗari tara da sittin da takwas (1962-1968), Léopold Sédar Senghor ya yi wasu kurakurai a siyasa waɗanda suka haddasa wasu ƙungiyoyin da suka yi masa bore.

A shekarar Alif da Ɗari Tara da Sittin da Takwas (1968) ne masana da ɗalibai masu alaƙa da aƙidar masanin falsafan nan wato ‘Karl Max’ suka juya masa baya.An Karrama Léopold Sédar Senghor sosai a duniya, ya karɓi kyaututtuka da lambobin yabo da dama. Daga ciki akwai lambar da Faransa ta ba shi matsayin da ake bai wa haziƙan sojoji.

Akwai ma kyautar marubuta ta Jamus wato ”German Book Trade” da kuma wasu digirin girmamawa masu yawa da wasu fitattun jam’i’on duniya suka ba shi.Staatspräsident von Senegal Senghor Besuch in Frankfurt am Main.

Wurare da cibiyoyi ma yanzu na amsa sunan Léopold Sédar Senghor. Daga ciki akwai filin jirgi da na wasanni na Senegal da Jami’ar nazarin harshen faransanci a birnin Alexandria na ƙasar Masar da gidauniyar Léopold Sédar Senghor, sai kuma cibiyar Senghor da ke a ƙasar Fotugal.

Wannan labarin ya samu ne tare da tallafin bayanan kimiyya da kuma na tarihi daga masana irin su; Farfesa Doulaye Konaté da Dakta Lily Mafela, da Farfesa Christopher Ogbogbo.

1 COMMENT

Leave a Reply