Ladi Kwali, fitacciyar me ƙera tukwane da hotonta ke kan Naira Ashirin

1
458

Hoton Ladi Kwali, ya bayyana a bayan takardar Naira Ashirin (₦20), kuma ita kaɗai ce sananniyar mace a kan takardar naira ta Najeriya.

An haifi Hadiza Ladi Kwali, a shekarar Alif da Ɗari Tara da Ashirin da Biyar (1925), a ƙauyen Kwali da ke yankin Gwari a Arewacin Najeriya. A can, sana’ar tukwane sana’a ce da ta zama ruwan dare a tsakanin mata, don haka ta koyi sana’ar ne daga wajen goggon ta, ta hanyar amfani da hanyar gargajiya.

A shekarar Alif da Ɗari Tara da Hamsin da Huɗu (1954), ta shiga Cibiyar Koyar da Tukwane na ‘Cardew’ a Abuja. Ita ce kaɗai mace mai koyon haɗa tukwane a wannan cibiyar, kuma ta kasance ɗaya daga cikin manyan ƙwararrun yin tukwane a Najeriya.

An sanya ta cikin mamba na ‘Order of the British Empire’ (MBE), ta kuma samu digirin digirgir daga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, a shekarar Alif da Ɗari Tara da Saba’in da Bakwai (1977).

KU KUMA KARANTA: Albufeira, ƙauyen kamun kifin da ya zama baban wurin hutu a duniya

Ta samu lambar yabo ta ‘National Order of Merit Award’ a Alif da Ɗari Tara da Tamanin (1980), da kuma lambar girmamawa ta ƙasa, wato Jami’ar Umarni ta Najeriya, (OON), a shekarar Alif da Ɗari Tara da Tamanin da Ɗaya (1981).

An canja sunan Cibiyar Koyar da Tukwane na ‘Cardew Pottery’ a Abuja, zuwa ‘Ladi Kwali Pottery’ an kuma sanyawa wani babban titi da ake kira ‘Ladi Kwali Road’ a Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.

Haka zalika, Ladi Kwali ta koyi ƙerar tukwane ne a wurin ƙanwar mahaifiyar ta tun ta na ƴar ƙarama, kuma ta samu horar wa mai kyau a wajen ƙanwar mahaifiyarta ta, inda ta ƙware sosai wajen ƙirar tukwanen.

Wannan dalilin na ƙwarewar ta ta ya sanya da zarar ta haɗa tukwanan nata kafin ranar kasuwa ta zagayo an sai da tukwanan.

Ta yi sanadiyar wani baturen Ingila mai ɗaukar hoton abubuwan ban mamaki mai suna Mikheal Cardew, Ladi Kwali ta yi su na sosai a duniya a shekara ta Alif da Ɗari Tara da Hamsin (1950).

A shekara ta Alif da Ɗari Tara da Hamsin da Ɗaya (1951), aka naɗa Mikheal Cardew a matsayin Mai Kula Da Ƙera Tukwane, a Ma’aikatar Kasuwanci Da Masana’antu, inda ya kafa makarantar Ƙera Tukwane a Abuja, ya kuma jawo Ladi Kwali a matsayin mai horar da ɗalibai a shekarar Alif da Ɗari Tara da Hamsin da Biyu, zuwa Alif da Ɗari Tara da Sittin da Bakwai (1952-1967), wato sun shafe shekaru Goma Sha Biyar ke nan su na koyar da tukwane a wannan makarantar.

Saboda kyawun tukwanen da Ladi Kwali ke ƙera wa da kuma sunan da suka yi gami da ingancin su ya sa sarkin Abuja na wannan lokacin Sulaiman Barau, ya sa ta ƙera masa tukwanan don ya ƙayata cikin fadarsa da su.

Ladi Kwali da Michael Cardew sun tafi ziyara ƙasar Ingila da Amurka, inda yake nuna ayyukanta kuma ya ja hakulan mutane da dama a ƙasashen biyu.

Shahararriyar a ƙera tukwane Ladi Kwali ta samu lambobin yabo da dama kamar haka;

A shekarar Alif da Ɗari Tara da Sittin da Biyu (1962) an karrama Ladi Kwali da MBE, wato [Member of the Oder of the British Empire].

A shekara ta Alif da Ɗari Tara da Saba’in da Bakwai (1977), Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya ya bata digirin girmamawa na Dakta wato, [Honorary Doctorate].

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta karramata da Lambar yabo mafi girma na Ilimi, wato, “Nigerian National Oder of Merit Award.”

A shekarar Alif da Ɗari Tara da Tamanin da Ɗaya (1981), Ladi ta samu Lambar yabo ta OON, wato, ‘Office of the Oder in the Niger.’

An sanya hotonta a bayan Naira Ashirin na kuɗin Najeriya, kuma ita ce mace ta farko da aka sanya hotonta a jikin kuɗi a Najeriya.

An sanya sunanta a wani babban layi da ke birnin Abuja mai suna, “Ladi Kwali Street.”

Hajiya Hadiza Ladi Kwali, ta rasu a ranar Goma Sha Biyu ga Watan Agusta, na shekarar Alif da Ɗari Tara da Tamanin da Huɗu (1984), ta na da shekaru Hamsin da Tara a duniya.

1 COMMENT

Leave a Reply