Kungiyar YWM Rigasa Ta Gudanar Da Taron Wayar Da Kan Al’umma Bisa Cancantar Sanata Uba Sani

0
1056

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

WATA kungiyar mata da matasa dake tafiyar Uba Sani Youth and Women Movement (YWM) ta dake Gundumar Rigasa Kaduna, ta gudanar da taron bayyana kudirinta na neman goyon bayan al’umma domin kara marawa Dan takararta mai neman Kujerar Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Malam Uba Sani, a karkashin Jam’iyyar APC mai mulki.

Taron wanda ya gudana a garin Rigasa Kaduna a ranar Asabar din daya gabata, an shirya shi ne da zummar wayar da kan al’ummar Gundumar bisa cancantar zaman Dan takarar Kujerar Gwamnan, kasancewarsa mutum wanda yake da manufofi da kudirin ganin ya kawowa al’ummar yankin nasara da ci gaba.

Da yake jawabi a wajen taron, Kodinetan mazabar Shiyyar Kaduna ta tsakiya na Sanatan mai ci, Kwamared Abubakar Rabiu Abubakar, ya bayyana cewa babu wani dan takarar da ya cancanci samun Kuri’un al’ummar yankin fiye da Sanata Uba Sani, domin a duk halin da ake ciki, yana tare da al’ummar dari bisa dari.

Ya kara da cewa, a cikin mukamai uku da Sanatan ya fara badawa yayin da ya ‘dane kan karagar mulki, Dan Gundumar Rigasa na daya daga cikin mutanen da aka fara ba mukami a karkashin shi ba tare yasan kowane ne shi, kana duk wasu kudirorin da yake gabatarwa a majalisar Tarayyar Najeriya, Gundumar Rigasa na daya daga cikin wuraren da ya ke kokarin ganin an kawo ci gaba domin ganin ta bunkasa.

Ya ce “Dan takarar Gwamnan Sanata Uba Sani, ya kasance mutum ne mai kishin al’ummar Gundumar Rigasa wanda hakan ne yasa da aka buƙaci karin Asibitin kiwon Lafiya na Tarayya wato Federal Medical Centre (FCM), guda uku, ya sanya sunan garin Rigasa a ciki domin samun wannan ci gaban, kana ya gina wajen wasannin motsa jiki saboda matasa.”

“Ya kamata mu aje banbancin akida na Siyasa mu marawa duk wani Dan garin Rigasa baya, kana mu zabi Shugabanni Nagari wadanda ke da zuciyar tallafawa Gundumarmu ta Rigasa domin ci gaban al’ummarmu, don haka muke rokon iyayenmu mata da maza, yayyanmu da kannenmu, abokai, da sauran al’umma da su dubi irin kyakkyawar manufar Sanata Uba Sani wajen tabbatar da sun zabe shi a zabe duka gari mai zuwa ta shekarar 2023 idan Allah Ya kaimu.”

Acewarsa, kasancewar Gundumar na daya daga cikin wuraren da suka bashi Kuri’unsu mafi rinjaye yayin neman zama Sanata, Dan takarar Gwamnan na da manufofi da kudirori kyawawa na ganin cewa Gundumar ta Rigasa ta samu duk wata damar samun ci gaba ta hanyar samar da abubuwan more rayuwa da inganta rayuwar al’ummar.

Tunda farko, Shugaban Kungiyar ta (Uba-YWM), Honarabul Aliyu Mu’azu, ya bayyana makasudin gudanar da taron a matsayin wata dama domin wayar da kan al’ummar Gundumar bisa kyawawan ayyukan da Dan takarar Gwamnan ya yi a matsayinsa na Sanata wanda mafi yawan al’ummar yankin basu sani ba.

Aliyu Sabo, ya kara da cewa yin hakan ya zama masu wajibi ne su fito su fadawa al’ummar yankin irin nasarorin da ci gaban aka samu ta hanyar Sanatan mai wakiltar Shiyyar Kaduna ta tsakiya a zauren majalisar Dattawa, shi yasa ita wannan Kungiya tasu mai albarka da tarin al’umma magoya suke kokarin ganin sun bi gida-gida sun sanar da Jama’a abubuwan alkhairin da ya yi.

A Karshe Shugaban Kungiyar, Honarabul Aliyu Mu’azu, ya shawarci al’ummar Gundumar da kada su bari a yaudaresu da dan wani abun da bai taka kara ya karye ba domin yin zaben tumun dare bayan ga zaahirin abin da suke gani na ayyukan alheri Sanata Uba Sani, domin hakan na iya zamar musu wani aikin da-na-sani a nan gaba.

Leave a Reply