Kungiyar AFAN Reshen Jihar Jigawa Ta Na Da Shugaba Nagari

0
323

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

AN bayyana cewa kungiyar manoma ta kasa reshen Jihar Jigawa ta na da shugabanni nagari wadanda kuma suke da kishin mnoman jihar kamar yadda ake gani a kowane lokaci.

Wannan bayani ya fito ne daga jami’in hulda da jama’a na biyu na kungiyar watau PRO II Malam Hussaini Mahmoud Dutse a wani sako da ya gabatar ga wakilin mu, inda ya nunar da cewa AFAN reshen jihar Jigawa tana cimma kyawawan nasarori wajen bunkasa kungiyar a fadin jihar.

Malam Hussaini Dutse ya kara da cewa shugaban kungiyar Alhaji Idris You Mai Unguwa yana kokari sosai domin tabbatar da cewa manoman jihar Jigawa suna samun ci gaba a sana’ar su ta noma tareda kyautata dangantaka tsakanin kungiyar da gwamnatin jihar wanda hakan abin alfahari ne ga daukacin manoman jihar.

A karshe, Malam Hussaini Mahmoud Dutse ya jaddada cewa kungiyar ta AFAN reshen jihar Jigawa zata ci gaba da yin aiki da manufofin ta wajen kawo managarcin ci gaba tareda bunkasa noma don wadata kasa da abinci, sannan ya yabawa sauran shugabannin kungiyar na matakin jihar da kanann hukumomi saboda kokarin da ake yi batare da gajiyawa ba.

Leave a Reply