Ku Gargadi Jami’in Ku Ya Kiyayi Yunkurin Raba Kan ‘Yan Jaridun Kaduna, NUJ Ta Buƙaci PDP

0
627

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

KUNGIYAR ‘yan Jaridu ta Najeriya (NUJ), reshen Jihar Kaduna, ta bukaci Jam’iyyar PDP Kaduna da ta gargadi Jami’in hulda da Jama’a (PRO), na Jam’iyyar Mista Katoh Alberah, bisa kokarin da ya ke na yunkurin raba kan ‘yan jaridun Kaduna.

Hakan ya biyo bayan matakin da Jami’in ya dauka na baiwa wasu ‘yan jaridu ‘yan kadan damar gudanar da aikin zaben fidda gwani na takarar gwamna a jam’iyyar PDP wanda ya ke aiki ne na kasa baki daya kuma ya ke da nasabar gurgunta aikin ma’aikatan a Jihar.

Kungiyar, ta sanar da bada matakin yin gargadin ne a cikin sanarwar da ta fitar ranar Laraba bayan kammala taronta na wata-wata da aka gudanar a Kaduna.

A cikin sanarwar mai dauke da sa hannun Usman Sani, Kungiyar ta dauki matakin da Jami’in ya dauka a matsayin wani yunkuri na haifar da baraka da rashin hadin kai a tsakanin mambobinta.

Sanarwar ta kuma yi tir da dabi’un da Jami’in Alberah me nunawa Yan Jaridun na rashin girmama da kaskanci ga ‘yan jaridar Kaduna.

Don haka kungiyar ta umurci mambobinta da su kara hada kai da kuma sadaukar da kansu wajen gudanar da ayyukansu, kada su bari wani mutum ko kungiya ta raba su.

Sanarwar ta ci gaba da cewa, “Idan har Jami’in ya ci gaba da bin wannan mataki na kokarin raba kan hadaddiyar kungiyar NUJ ta Kaduna, to kungiyar ba za da wani zabi face wanda ya wuce ta kauracewa ayyukan Jam’iyyar a jithar.”

Don haka kungiyar ta yi Allah-wadai da yadda jami’an tsaro su ka muzgunawa mambobin kungiyar a wani lamari na baya-bayan nan a sakatariyar jam’iyyar ta PDP yayin gudanar aikinsu.

Leave a Reply