Kotu ta yanke wa wasu ‘yan Ghana masu safarar wiwi zuwa Najeriya, hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan yari

1
487

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA) ta damƙe wasu ‘yan ƙasar Ghana 9 bisa laifin yunƙurin shigo da tabar wiwi kilogiram 10,843.95 zuwa Najeriya.

Mai shari’a Akintayo Aluko na babbar kotun tarayya da ke Legas a lokacin da yake yanke hukunci a kan lamarin, ya samu ‘yan Ghanan da laifin haɗa baki da kuma safarar tabar wiwi.

‘Yan Ghanan sun yi yunƙurin safarar tabar wiwi ta cikin teku inda aka yanke musu hukuncin ɗaurin shekaru 72 a gidan yari.

Rahotanni da dama sun nuna cewa tun da farko wasu jami’an hukumar tsaro ta Civil Defence ne suka kama su kuma aka tura su NDLEA domin ci gaba da bincike da gurfanar da su gaban kuliya.

Bayan binciken, an gano cewa an gurfanar da su gaban kotu mai lamba FHC/L/292C/2021. Waɗanda aka yanke wa hukuncin sun haɗa da; Victor Wuddah, Freeman Gazul, Adotete Joseph, Sottie Moses, Sottie Stephen, Christian Tette, Kanu Okonipa, Daniel Koyepti, and Kanu Natte.

1 COMMENT

Leave a Reply