Kisan Direba Ya Jawo Zanga-zanga A Yobe

0
333

..

Daga Rabo Haladu

Matasa da dama ne suka fito zanga-zanga a Garin Gashua da ke Jihar Yoben  bayan zargin da ake yi na soja ya harbe direban mota a wani gidan mai.

Wasu da suka shaida lamarin sun shaida  cewa da yammacin Juma’a ne sojoji suka zo wucewa ta wani gidan mai da ke garin Alkali wanda ke da nisan kilomita biyar daga garin Gashua.

A cewarsu, ko da sojojin suka zo sai suka ce kada kowa ya gudu, sai wani matashi da ke tuƙa babbar mota ƙirar ‘zul’ ya ji tsoro ya gudu wanda hakan ne ya sa ɗaya daga cikin sojojin ya harbi matashin.

Bayan harbin matashin, an garzaya da shi asibiti saboda rauni mai tsanani da ya samu amma a asibiti ya cika, kamar yadda aka shaida.Mazauna garin sun bayyana cewa akwai dokar da sojojin suka saka a yankin na cewa kada a kuskura a rinƙa sayar da mai a cikin jarka ko durum sakamakon suna zargin ana kai wa mayaƙan Boko Haram ne, wanda a ganinsu hakan ne ya sa sojojin suka je gidan man.

Ganin cewa wanda aka kashen ɗan asalin garin Gashua ne, sai matasan garin suka fusata inda suka bazama kan tituna domin nuna ɓacin ransu inda suka ƙona tayoyi.

Rahotanni sun bayyana cewa duk wasu manyan allunan kan titi a Gashua matasan sun ƙona su da lalata su inda suke faɗan kalaman cewa “ba ma so, sojoji suna cutar mu”.

ta tuntuɓi mai magana da yawun ƴan sanda reshen Jihar Yobe ASP Dungus Abdulkarim inda ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya bayyana cewa tuni sun kwantar da tarzomar da aka tayar.

ASP Dungus ya bayyana cewa sun lallaɓi matasan da suka fusata da su yi hakuri inda ya ce wasu daga cikinsu sun fahimta sun koma gidajensu, amma ya ce waɗanda suka yi taurin kai sun fatattake su.

Haka kuma ya bayyana cewa ba su kama ko mutum guda daga cikin masu zanga-zangar ba kuma jami’ansu na ci gaba da shawagi domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Shi ma Gwamnan Jihar Yobe Mai Mala Buni ya yi kira da matasan na Gashua da su yi hakuri su rungumi zaman lafiya.

A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Mamman Mohammed ya fitar, gwamnan ya bayar da umarni a gudanar da bincike kan lamarin da kuma daukar mataki

Kisan direba’ ya jawo zanga-zanga. a jihar yobe

Leave a Reply