Connect with us

Tarihi

Kayan masarufi da gargajiyar Arewa (kashi na ɗaya)

Published

on

MAFICI;

Na’ura ce ta gargajiya da ake amfani da shi wajen samar da iska. Ana fifita da shi domin samun sanyin jiki a lokacin zafi ko kuma fifita abinci domin ya yi saurin hucewa da sauransu.


Mafici

KASKON TURARE;

Kaskon turare na ɗaya daga cikin kayayyakin amfani da masu sana’ar ginin tukwane suke samarwa a ƙasar Hausa. Ana zuba garwashin wuta a cikinsa domin ƙona turaren ƙamshi wadda aka fi sani da turaren wuta.

Kaskon turaren wuta

LUDAYI

Abin amfani ne da ake samarwa daga duma, ana shan kunu, fura, koko da sauran dangogin abubuwan sha da ake ɗebowa daga ƙwarya ko ƙoƙo ta hanyar amfani da ludayi. Girman ludayi ya bambanta, mafi girma shi ake kira makamfaci.

Ludayi

FITILA

Kafin amfani da fitilun lantarki, hasken rana, batura, da sauran nau’ukan zamani, fitilun Kananzir da aka fi sani da Fitilar ƙwai a ƙasar Hausa, ta na samar da wadataccen haske a lokacin amfani. An yi amfani da ita na tsawon lokaci.

Fitilar ƙwai

Fitilar ƙwai ta na da tasiri sosai musamman da dare. A kan zuba Kananzir a ciki sannan kuma akwai ƙullin lagwani wadda ta shi ne haske ya ke yin togo. Har ila yau, akwai majuyin daidaita haske wadda za iya rage hasken ko kuma ƙari.Tare da sabbin fasahohin zamani, mutane da dama ba sa yin amfani da fitilun ƙwai a wannan lokaci.

RANDA

Randa, ta kasance firiji na gida a wancan lokacin, an yi ta ne saboda ajiye kayan lambu, da sanyaya ababen sha domin kar su lalace, sannan a kan zuba ruwan sha a ciki musamman lokacin zafi domin ya kasance sassanya kuma tsaftatacce.

Randa

Ana yin ta ne da ƙasa, sannan ta na sanyaya da kuma adana abinci da abin sha. Har yau, ana amfani da ita a wasu wurare, musamman a karkara.

TSANA

Tsana tsohuwar riga ce ta mata da al’ummar Lala da ke gundumar Gombi ke amfani da ita.Al’ummar Lala, na zaune ne a ƙasar gargajiya ta jihohin Adamawa da Borno da ke Arewa Maso Gabashin Najeriya.Su na zaune a cikin karkara ne, in da galibin mutanen ke yin noma da kiwon dabbobi.

Tsana

Noma dai ita ce babbar sana’ar da al’ummar Ƙaramar Hukumar Gombi ke yi, tare da noma irin su Gero, da Dawa, da Alkama, da Masara, da ake nomawa a yankin.

Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Tarihi

Tarihin wasan Haɗejawa da Katsinawa

Published

on

Tarihin wasan Haɗejawa da Katsinawa

Tarihin wasan Haɗejawa da Katsinawa

Daga Ma’azu Hamza Hadejia

Ɗalibai suna ta min tambaya akan tarihin asalin wasan Haɗejawa da Katsinawa sai naga ya kamata yau na bada wannan amsar.

Masarautar Katsina ba makwabciyar Haɗeja bace, tana da ɗan nisa da ita, daga arewa maso yamma (Northwest). Dukkan su Habe sun mulke su kafin Jihadi ya haɗa su cikin Daular Sakkwato.

Akwai kyakkyawar danganta ta wasanni tsakanin al’umomin Masarautun guda biyu wacce ta kullu shekara da shekaru..Akwai bayanai daban-dabam da ake jingina su a matsayin dalilan da suka kawo wannan dangantakar, kuma dukkan su suna da harshen damo.

Dalili na farko an danganta shi da wasan dangi. A karkashin wannan ajin akwai kaulin da yayi bayanin cewa asalin waɗanda suka kafa Haɗejia da Katsina maharba ne.

Lokacin da suke yawan harbin su har suka kawo ga yankin Hadejia, sai wasu daga cikin su zauna zama na dindindin, saboda ganin irin ni’ima da dausayin wurin.

Ragowar sai suka zarce har suka zo yankin Katsina, suka zauna. A dalilin su jama’a ta karu har aka sami Sarauta. Duk da nisa tsakanin waɗannan ‘yan uwa, sun cigaba da mu’amala har ake ce wani ɗan Sarkin Haɗeja ya aure diyar Sarkin Katsina.

Wannan al’amari ya faru shekaru da dama kafin Jihadi, wato lokacin mulkin Habe.

Wani ƙaulin kuma yana jingina dalilin samuwar dangantakar wasannin ga Fulanin da suka Jagoranci Jihadi a yankin Haɗeja da Katsina. Wannan bayani ya nuna cewa dukkan su ‘yan uwan juna ne, kuma tare suka yi kaura zuwa yankin Katsina.

Ardo Abdure da jama’arsa sun zauna a ɓangaren Kankiya kafin daga baya su yi kaura gabas har suka iso yankin Haɗeja suka zauna. Sun cigaba da hulɗa tsakaninsu har aka yi Jihadi suka kasance shugabannin Masarautun guda biyu.

A ɗaya hannun wasu suna jingina asalin wasannin ga yaƙi tun a lokacin mulkin Habe. Wani ƙaulin yace akwai lokacin da Sarkin Katsina na wannan zamanin ya daura yaƙi zuwa Haɗeja, kafin ya ƙaraso cikin ƙasar Haɗeja ya yada zango a cikin ƙasar Gumel.

Sarkin Haɗeja ya samu labarin zuwan Sarkin Katsina, saboda haka sai ya tada wani daga cikin Jarumansa domin yaje ya gano irin shirin Katsinawa.

KU KUMA KARANTA: Ɗan Ghana ya kafa tarihi na rungumar bishiyoyi a duniya

Wannan Jarumi na Haɗeja yayi kyakkyawan shiri ya kama hanya ya isa sansanin abokan gaba da dare. Ba tare da wani ya ganshi ba, kai tsaye ya wuce tantin Sarki ya sake shi da wata kuyangarsa suna barci..

Nan take ya kwance wandon Sarkin Katsina ya daurawa kuyangar, ya kuma cire dan kwalin kuyangar ya daurawa Sarki, a wani ƙaulin ya daidaita wuka Sarki yayi tafiyarsa ba tare da ya cutar da su ba.

Da gari ya waye Sarki ya farka yaga abin da aka yi musu, ya tabbatar ban da Haɗejawa ba mai yi masa wannan, sai ya yanke hukunci cewa lallai sunfi karfinsa. Saboda haka ya juya akalar yaƙi ya koma gida.

Wani ƙaulin kuma yace lokacin da wannan Sarki na Katsina ya iso Gumel, kan hanyarsa ta yakar Haɗejia, Sarkin Gumel ya shawarce shi da ya janye wannan aniya tasa, kuma ya yarda ya janye.

A lokacin kuma Haɗejawa sun sami labarin fitowar Sarkin Katsina har sun gama shiri tsaf suna sauraron isowarsa sai suka ji shiru.

Wani ƙaulin yace Haɗejawa ne suka tunkari Katsinawa da yaƙi, suka bi ta Daura. Yayin da suka yi kusa da Katsina, sai suka fahimci Katsinawa ba kanwar lasa bace, saboda haka suka janye suka dawo gida.

Daga waɗannan bayanai na dalilin dangantakar wasannin tsakanin Haɗejawa da Katsinawa za’a iya fahimta cewa koda akwai ‘yan uwantaka, anfi bada karfi akan dalilin yaƙin da ba’a yi shi ba.

Continue Reading

Al'ajabi

Tarihin Rijiyar Bozundalla wadda ta yi shekaru sama dubu ba taɓa ƙafewa ba

Published

on

Daga Ibraheem El-Tafseer

Rijiyar Bozundalla da ke garin Wawa na ƙaramar hukumar Funakaye ta jihar Gwambe, rijiya ce mai ɗimbim tarihi da abubuwan al’ajabi. Garin Wawa, wani gari ne dake kusa da babban birnin Bajoga, hedikwatar ƙaramar hukumar Funakaye a jihar Gwambe. Daga Bajaoga za ka yi tafiyar kilomita 15, zuwa kwanar Baffaru, to a nan za ka hau mashin zuwa garin Wawa.

Garin yana lungu sosai, indai ba ranar kasuwar garin ba, to ba kasafai ake samun mota zuwa garin ba, dole sai dai a hau mashin. Idan ka hau mashin za’a yi ta falfala gudu da kai a cikin ƙungurumin daji. Duk da akwai kwalta, amma kwaltar da ita da babu duk ɗaya, domin kuwa kwaltar ta mutu murus. Haka za ku yi ta faɗa wa ramuka, manya da ƙanana. Sai kun yi tafiyar kusan awa ɗaya, kafin ku isa garin Wawa. Garin Wawa, gari ne na ƙabilun Bolawa, garin yana da matsakaicin girma da jama’a hululu.

Cikin daji za ku yi ta nausawa, amma a hanya akwai garuruwan Biri guda biyu. Wato Birin Fulani da Birin Bolawa, suna maƙwabtaka da juna.

Wakilin Neptune Prime, Ibraheem El-Tafseer ya yi tattaki har zuwa wannan gari don tattaunawa da Dagacin garin na Wawa, don jin haƙiƙanin tarihin wannan Rijiya ta Bozundalla mai ɗimbim tarihi da abubuwan al’ajabi.

KU KUMA KARANTA:Shugaba Tinubu ya taya kiristoci murnar bikin Ista

Ga yadda tattaunawar ta su ta kasance;

NEPTUNE HAUSA: Yallaɓai, da farko muna so ka gabatar da kanka a masu karatunmu?

DAGACIN WAWA: Suna na Alhaji Abubakar Sadik Lawal. Ni ne Dagacin wannan gari na Wawa.

NEPTUNE HAUSA: Muna so ka bayyana mana tarihin wannan Rijiya ta Bozundalla?

DAGACIN WAWA: Wannan Rijiya tana da tarihi mai yawan gaske, sai dai zan gutsira muku ɗan abin da ya samu. Asalin wannan Rijiya ta shafe shekaru sama da dubu kuma babu wani mutum ɗaya da zai ce shi ne ya tona ta. Sai dai an sabunta ta shekaru saba’in da suka gabata. Sakamakon zabtarewa da wani ɓangare na Rijiyar ya yi, sai Sarkin wancan lokacin, ya sa aka yi gayya irin na mutanen mu (Bolawa), aka ɗebo itacen ƙiryoyi, to waɗannan itatuwan ƙirya ɗin aka ɗaure ta, kamar yadda ka leƙa ka gani. Babu Siminti ko kaɗan da aka ɗaure ta da shi.

Asalin yadda aka samu wannan Rijiya ba mutum ba ne ya samo ta, dabba ce ta gano ta. Akwai dabba irin ta mu ta fada, wato Goɗiya (ta macen Doki). Yadda abin ya faru shi ne, ita wannan ta macen Dokin, kullum aka dawo daga kiwo aka ba ta ruwa ba ta sha. To sai wannan mai Dokin ya damu matuƙa akan me ya sa idan an ba ta ruwa ba ta sha?

To sai wannan mai Dokin ya yi wata hikima, ya ƙira wasu mutane daga fada, suka bi bayan wannan Dokin bayan ta gama kiwo. Sai aka ga ta shiga cikin wata duhuwa ta bishiyoyi, sai suka laɓe suna kallon ta. Bayan ‘yan mintuna, sai suka ga Dokin ta fito. Da suka leƙa inda ta shiga ɗin, ashe ruwa ne a kwance malala a wajen. To wannan shi ne asalin gano wannan Rijiya. Ruwan ta ƙarƙashin duwatsu yake ɓulɓulowa.

Ita wannan Rijiya tana da suna, ana ce mata Bozundalla, kalma ce ta Bolanci. Dalla ana nufin tsakiya. Bozundalla ana fassara shi da tsakiyar gari, amma ka ga inda Rijiyar take ba tsakiyar gari ba ne. Amma a wancan lokacin nan ne tsakiyar Ganuwa da Ganuwa. Tsakiyar gari ɗin kenan a wancan lokacin. Wawa tana da Ganuwa guda uku. To ka ji yadda aka samo wannan Rijiya.

NEPTUNE HAUSA: Da yake an san Rijiyoyi da ƙafewa, wasu ma sai an musu yasa, ko wannan Rijiya ta taɓa ƙafewa?

DAGACIN WAWA: Wannan Rijiya ba ta taɓa ƙafewa ba, sama da shekaru dubu. A tarihi dai mun tarar da iyayenmu da kakanninmu da iyayen kakanninmu, duk haka suka ganta, kuma haka suka tafi suka barta, ba taɓa ƙafewa ba. Amma a shekaru kamar 70 da suka gabata, an sabunta ta, saboda yau da kullum ana ɗiban ruwa a cikinta, to akwai itatuwa na sama-saman kan Rijiyar, waɗanda aka ɗaure kan Rijiyar da su, sun ciccire. Shi ne aka yi gayya, aka ƙira ‘yan’uwanmu Bolawa na nesa da na kusa, aka taru aka rufe saman Rijiyar. Aka sake shirya musu itatuwan kamar yadda suke a da can.

Ita dai wannan Rijiya an ɗaure ta ne da itatuwan ƙirya tun daga jikin duwatsun da ruwan yake ɓulɓulowa, har zuwa sama. Kuma ruwa a wannan Rijiya bai taɓa ƙafewa ba, tun daga wancan lokacin da aka gano ta har zuwa yau ɗin nan da nake hira da kai.

Wannan Rijiya tana da zurfin gaba 16, duk gugar da muke zarawa a ɗebo ruwa, tsayinsu gaba 16, kuma ba mu taɓa ƙarawa ba. Kuma awa 24 ake ana ɗiban ruwa a cikinta. Kuma za ka samu mutane sama da 50 kowa ya zara gugarsa yana ɗiban ruwa a ciki.

NEPTUNE HAUSA: Yaya daɗin wannan ruwa yake, yana da zartsi ne, ko gishiri-gishiri ko kuma kanwa-kanwa da aka san ruwan wasu rijiyoyi da shi?

DAGACIN WAWA: Ruwan wannan Rijiya, ruwa ne mai daɗin gaske. Ba don Azumi ba, da kasha ka ji da bakinka. Amma tun da ka ɗiba idan an sha ruwa za ka gaskata zance na.

Mu mun ji labari daga wajen kakanninmu cewa, wannan Rijiya tana haɗe ne da kogin Gashinge da ke ƙaramar hukumar Nafaɗa ta jihar Gwambe. Ko waye ka tambaya a yankin Nafaɗa zai nuna maka bakin rijiyar Wawa, wanda ake ce masa ‘Bobuzum Wawa’.

A wancan lokacin akwai Sarkin ruwa, da ya zo nan, ya ce kwale-kwalensa ya ɓata, kuma yana cikin wannan Rijiyar. Aka yi ta mamaki. Ya ce shi dai a ba shi izini zai shiga ya fito da kwale-kwalensa. Sarkin Wawa na wancan lokacin ya ba shi izini ya shiga. Ya shiga rijiyar shi da Karensa. To sai Sarkin ya tura mutane a kan Dawakai, a kan su je can Gashinge ɗin su jira su ga fitowarsa. Ai kuwa suna isa can, sai ga shi, sun iso tare. Sarkin ruwan sai ga shi ya fito tare da kwale-kwalensa. To wannan shi ne ya tabbatar mana da cewa wannan Rijiya tana haɗe da kogin Gashinge na ƙaramar hukumar Nafaɗa.

NEPTUNE HAUSA: Ganin yadda mutane sama da 50 suke cike a kan wannan rijiya kowa yana ɗiban ruwa, ko wani ya taɓa faɗawa wannan rijiya ya mutu?

DAGACIN WAWA: Wannan rijiya ba ta taɓa kashe kowa ba. Asali ma babu wani mutum da ya taɓa faɗawa wannan rijiya, kuma ba dare ba rana ake ɗiban ruwa a wannan rijiya, amma babu wanda ya taɓa faɗawa.

NEPTUNE HAUSA: To ko akwai wani sirri da ruwan wannan rijiya yake da shi? Ma’ana yana maganin wani abu idan an sha?

DAGACIN WAWA: (Dariya). Wannan abarwa Allah kawai. Ba komai za mu bayyana wa duniya ba.

NEPTUNE HAUSA: Akwai wani ƙalubale da kuke fuskanta game da wannan rijiya ko wannan gari?

DAGACIN WAWA: Babban ƙalubalenmu a wannan gari shi ne matsalar ruwan sha. Ka gani da idonka yadda jama’a suka yi ɗafifi suna ta ɗiban ruwa a wannan rijiya. To ita kaɗai ce take ba da ruwa, duk rijiyoyin garin sun ƙafe. Ko an tona rijiya to daga baya ƙafewa take. Wannan ce kaɗai ba ta ƙafewa, shi ya sa ka ga an mata wannan tururuwa ɗin ana ta ɗiban ruwa.

Yanzu a wannan gari, jarkar ruwa ɗaya Naira ɗari biyu ce. A ƙauyuka na kusa da mu kuwa, har Naira ɗari biyar ake sayarwa. Akwai motoci da suke zuwa garin Biri suke ɗebo ruwa a irin babban tankin nan da ake ɗorawa a saman gida, to Naira dubu 50 suke sayar da tanki ɗaya. Lallai muna fuskantar babbar matsala na rashin ruwan sha a wannan gari. Kuma hakan yana da alaƙa da yawan da jama’ar da muke da su a wannan gari, ba kamar shekarun baya ba.

Don haka muna ƙira ga gwamnatin tarayya da gwamnatin jihar Gwambe, muna so a zo a inganta mana wannan rijiya mai ɗimbim tarihi, a saka ta a jerin wuraren ziyara na tarihin jihar Gwambe. Domin kuwa rijiya ce mai abubuwan al’ajabi da daman gaske. Sannan a zo samar mana da ruwan sha. Muna fuskantar matsala sosai a wannan gari na ruwan sha, kamar yadda na bayyana a baya.

NEPTUNE HAUSA: Mun gode.

DAGACIN WAWA: Ni ma na gode.

Continue Reading

Labari

Abubuwan da ba ku ji ba game da ƙasar Mozambik (Hotuna)

Published

on

Mozambik, ƙasa ce da ke kudu maso gabashin Afirka, ta na kuma da iyaka da Tekun Indiya daga gabas, Tanzania a arewa, Malawi da Zambiya a arewa maso yamma, Zimbabwe a yamma, da Eswatini da Afirka ta Kudu a kudu maso yamma.

Ƙasar ta na da babban teku da ke da mahimmanci ga tattalin arziƙin ƙasar da kuma rawar da yawon buɗe ido da kamun kifi ke taka wa wajen ci gaban ƙasar.

Ƙasar mai cin gashin kanta a halin yanzu, an raba wani yanki daga cikinta zuwa Comoros, Mayotte da Madagascar ta tashar ruwa na Mozambik da ke gabas.

Tsakanin ƙarni na 7 zuwa na 11, jerin garuruwan tashar jiragen ruwa na Swahili sun haɓaka a wannan yanki, waɗanda suka ba da gudunmawa ga haɓaka al’ada da harshen Swahili.

A ƙarshen zamanin da, ‘yan kasuwa daga Somaliya, Habasha, Masar, Saudi Arabiya, Parisa, da Indiya ne ke yawan zuwa waɗannan garuruwa domin fatauci.

Tsibirin Mozambik, wani yanki ne mai cike da murjani a gaɓar tekun ƙasar, kuma wani matsayi ne mai muhimmancin tarihi, inda al’adu daban-daban suka haɗu kuma suka bar tarihi a lokacin ɓullowa da bunƙasuwar hanyar cinikin teku tsakanin nahiyoyi a faɗin yankin.

Mozambik ta na da albarkatu masu tarin yawa, duk da cewa tattalin arziƙin ƙasar ya dogara ne a kan kamun Kifi, da noma tare da bunƙasa masana’antar abinci da abubuwan sha, masana’antar sinadarai, aluminum da man fetur. Sai dai kuma, ɓangaren yawon buɗe ido ya na ƙara faɗaɗa.

Yawan al’ummar ƙasar ya kai kusan miliyan 30, kamar yadda aka ƙiyasta a 2022, sun kuma ƙunshi ‘yan ƙabilar Bantu da dama.

Babban birnin ƙasar shi ne Maputo, wadda ya ke zama Fadar Gwamnatin ƙasar.

KU KUMA KARANTA: Jarirai na iya banbance sautin kalamai sa’o’i kaɗan bayan haihuwa

Haka nan, harshen hukuma ɗaya tilo a Mozambik shi ne harshen mulkin mallaka na Portuguese, wadda galibi ana magana da shi a cikin birane a matsayin harshe na farko ko na biyu, kuma gaba ɗaya a matsayin harshen gudanarwa na gwamnati.

Harsunan gida mafi mahimmanci sun haɗa da Tsonga, Makhuwa, Sena, Chichewa, da Swahili. Har ila yau, akwai kusan harsuna 46 da ake magana da su a cikin ƙasar, ɗaya daga cikin mafi shura shi ne, Língua de sinais de Moçambique.

Addini mafi girma a Mozambik shi ne, Kiristanci, tare da wasu tsiraru masu bin addinin Musulunci da kuma addinan gargajiya na Afirka.

Hukumar Kula da Adana Kayan Tarihi ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNESCO), ta lissafa tsibirin a matsayin ɗaya daga cikin wuraren tarihi na duniya a cikin shekara ta 1991.

Kalli hotunan a nan:

Continue Reading

GOCOP ACCREDITED MEMBER

You May Like