Kamfanin mai na Najeriya NNPC ya sanar da komawa aikin neman mai a yankin Tafkin Chadi da ke jihar Borno.
Kamfanin ya dakatar da aikin ne a watan Yuli na shekara ta 2017, bayan da wasu mahara da ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai wa ma’aikatan hari har suka yi garkuwa da wasu.
Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi ta intanet ga taron ƙaddamar da komawa kan aikin gano man a wata rijiya da ke yankin Wadi-B a garin Tuba na ƙaramar hukumar Jere.
KU KUMA KARANTA: A watan Yuli za mu fara samar da man fetur – Ɗangote
Bayan da yanayin tsaro ya inganta ne a shekara ta 2022 kamfanin ya yanke shawarar sake komawa aikin a rijiyar ta Wadi-B. Jaridar daily Trust ta ruwaito cewa a lokacin da daraktan zartarwa na ɓangaren aikin neman man a kamfanin na NNPC, Mukhtar Zanna, ya ce za a toni rijiyar zuwa zurfin ƙafa dubu 14.
Ya ce suna da ƙwarin gwiwa a kan aikin saboda suna da bayanai da kuma sabuwar fasaha ta zamani.
Kamfanin ya ce yana da kyakkyawan zato cewa za a samu mai da gas mai yawan gaske a wannan wuri.