Jarumin Kannywood, Karkuzu ya makance, yana kukan neman taimako

1
316

Fitaccen jarumin Kannywood, Abdullahi Shuaibu wanda aka fi sani da Karkuzu ya makance kuma yana fama da rashin lafiya.

Jarumin, wanda aka yaɗa bidiyonsa a shafukan sada zumunta, ya nemi taimakon kuɗi, inda ya bayyana cewa ya yi rashin lafiya tun watan Disambar 2020.

Shuaibu ya fara fitowa a masana’antar nishaɗantarwa ta Hausa a shekarun 1980 tare da shahararriyar wasan kwaikwayo mai suna Karkuzu na Bodara wanda ya sanya ake masa laƙabi da Karkuzu.

A zantawarsa da wannan jarida bayan faifan bidiyo, Karkuzu ya ce, “Yanzu na makance kamar yadda nake magana da ku. Ina matuƙar buƙatar taimakon kuɗi. Ba ni da abincin da zan ci da ciyar da iyalina.

KU KUMA KARANTA: Yadda mutuwar Alhaji Mala na shirin ‘Daɗin Kowa’ ta jijjiga Kannywood

“Gidan da nake zaune yanzu za a sayar. Idan sun sayar da wannan gidan, ban san inda zan dosa ba. Don haka ne nake neman taimako daga ‘yan Najeriya da su kawo min agaji.

A ƙalla ‘yan Najeriya su taimaka min sayan wannan gidan da nake zaune.”

Dangane da makanta, ya ce, “An min aiki sau biyu, amma a ƙarshe likitoci sun ce glaucoma ce, kuma ba zan sake gani ba. Na yarda da hakan a matsayin makoma ta. Amma ya kamata ‘yan Nijeriya su taimake ni. Kawo min gidan nan, da abinci.”

Masana’antar Kannywood na da ƙungiyoyi da dama, amma akwai zargin cewa ‘yan wasan kwaikwayo da dama ba sa kula da su idan ba su da lafiya kuma suna buƙatar taimako.

Zuwa haɗa wannan rahoto, ɗan wasan ƙwallon ƙafa na Najeriya Ahmad Musa ya ba shi kyautar naira dubu ɗari biyar, sannan ya ce a nemo gida na naira miliyan biyar zai saya masa.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here