Rahotanni daga Isra’ila na cewa ƴan sanda da masu bincike sun kai samame ofisoshin Al Jazeera da ke Birnin Ƙudus inda suka ƙwace kayayyakinsu na aiki.
Ministan sadarwa na Isra’ila Shlomo Karhi ne ya tabbatar da hakan jim kaɗan bayan gwamnatin Isra’ilar ta ɗauki matakin rufe ofisoshin na Al Jazeera a faɗin ƙasar.
Wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta ya nuna yadda jami’ai a cikin farin kaya suke kwance kyamarorin kafar watsa labaran a wani ɗakin otel wanda kafar ke amfani da shi a matsayin ƙwarya-ƙwaryan ofishi.