Isra’ila ta sanar da shirin ƙayyade adadin masu zuwa sallar Juma’a a Masallacin Al Aqsa

0
106

Isra’ila ta sanar da cewa za ta ƙayyade adadin Musulman da za su rinƙa zuwa Sallar Juma’a a Masallacin Al Aqsa a lokacin watan Ramadana.

Ministan ƴan sandan ƙasar ne ya sanar da hakan inda ya ce akwai yiwuwar masallacin ya kasance wurin da za a gudanar da zanga-zanga.

Ministan tsaron ƙasar Itamar Ben-Gvir a ranar Talata ya ce yunƙurin da ya yi na haramta wa akasarin Musulmai Sallar Juma’a hakan bai yiwu ba sakamakon Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi watsi da hakan.

Sai dai ya ce duk da hakan za a ƙayyade adadin mutanen zuwa mutum 40,000 ko 50,000.

Leave a Reply