Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta bayyana gwamna mai ci Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan jihar Adamawa.
INEC ta ayyana Fintiri a ranar Talata bayan ta ci gaba da tattara sakamakon zaɓen da aka yi a ranar Asabar. A sakamakon da INEC ta sanar, Fintiri ya samu ƙuri’u dubu 430,821 inda ya doke Aisha Binani ‘yar takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) wacce ta samu ƙuri’u 396,788.
Zaɓen gwamnan Adamawa ya ci karo da kura-kurai bayan da kwamishinan zaɓe na jihar, Hudu Yunusa-Ari, ya ayyana Binani a matsayin wanda ta lashe zaɓen yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaɓen.
KU KUMA KARANTA: An tsaurara tsaro a wajen ci gaba da tattara sakamakon zaɓe a Adamawa
INEC ta bayyana sanarwar da Hudu ya yi cikin gaggawa a matsayin rashin cancanta da kuma yin amfani da ƙarfin ikon.
Daga bisani an dakatar da REC na Adamawa tare da ba da shawarar a gurfanar da shi gabanin ci gaba da tattara sakamakon zaɓen a ranar Talata.
Da wannan sanarwar, Fintiri zai sake yin gwamnan jihar Adamawa a karo na biyu.
[…] KU KUMA KARANTA: INEC ta bayyana Gwamna Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa […]
[…] KU KUMA KARANTA: INEC ta bayyana Gwamna Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen gwamnan Adamawa […]