Hukumar hana fasa kwauri wato kwastam ta Najeriya ta naɗa Abdullahi Aliyu Maiwada a matsayin kakakin ta

0
451

Shugaban Hukumar ta kwastam Kanal Hameed Ibrahim Ali mai ritaya ya bada umarnin nada CSC Maiwada bayan duba nagarta da kuma iya aikinsa shekara da shekaru a hukumar.

Maiwada dai ya taɓa zama kakakin hukumar na shiyya ta biyu ta hukumar kwastam dake Kaduna ya kuma rike wannan mukami a jihar Ogun dake arewa maso yamma na tsawon shekaru.

KU KUMA KARANTA: Musulma ‘yar Arewa ta kafa tarihin zama mace ta farko a matsayin lauyan manyan kotunan Ingila da Wales

Ya dawo shalkwatar hukumar a shekarar 2020 inda ya zama jami’in hulɗa dake tsakanin gidan jarida na kwastam da jami’an kwastam a ɓangarorin Najeriya.

Maiwada yayi digirinsa na farko da na biyu a jami’ar Bayero ta Kano, a fannin Geography. Daga bisani ya ƙara yin digiri na farko da na biyu a fannin jarida a jami’ar Crescent dake jihar Abeokuta.

A yanzu yana digiri na uku a fannin jarida.

Leave a Reply