Hisbah ta kama mata 15 da suka halarci bikin ‘yan luwaɗi a Kano

3
345

Hukumar hisbah ta jihar Kano, ta kama wasu matasa 19 a wani taron biki da aka shirya a cikin birnin Kano bisa zarginsu da halartar wani shirin auren jinsi na ‘yan luwaɗi.

Rahotanni sun nuna cewa, waɗanda ake zargin da basu haura kimanin shekaru 20 na sun halarci taron domin shaida ɗaurin auren wasu da ake zargin ‘yan luwaɗi ne, mai suna Abba da Mujahid.

An ce jami’an hisbah sun kutsa kai wurin da lamarin ya faru kafin a fara bikin auren, inda aka cafke mata 15 da maza hudu.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin, babban kwamandan hukumar hisba ta Kano, Sheikh Haruna Ibn Sina, ya ce an kama su ne bayan rohoto da wani mazaunin yankin ya bayar.

Ya ce su biyun da aka yiwa laƙabi da ango da amarya, Abba da Mujahid, sun tsere ne bayan isowar jami’an hukumar.

KU KUMA KARANTA:Kotu ta yanke hukuncin kisa ga wasu ‘yan luwaɗi a Ningi

Babban kwamandan ya ce wacce ta shirya taron mai suna Salma Usman ‘yar shekara 21 ita ma ta tsare, ya ƙara da cewa hukumar za ta kara zage damtse wajen cafke ma’auratan da suka gudu.

Ya ce hukumar za ta mika waɗanda ke tsare ga ‘yan sanda domin ɗaukar matakin da ya dace, saboda yawancin matan sun yi ikirarin cewa an gayyace su ɗaurin auren ne daga jihohin makwabta.

3 COMMENTS

Leave a Reply