Hausawa da rubutun Hausa

1
126
Hausawa da rubutun Hausa

Hausawa da rubutun Hausa

Daga Yusuf Alhaji Lawan

Daga cikin tagomashi da Allah Ya yi wa Harshen Hausa, har da zamansa Harshen al’umma. Kasancewarsa Harshen da miliyoyin mutane ke amfani da shi domin sadarwa a tsakaninsu.

A Arewacin Najeriya, tare da cewa akwai Harsuna da dama, amma mafi yawan mazaunan wannan yanki sun fi amfani da Harshen Hausa wajen mu’amala ta yau da kullum.

A ƙasashen Nijar da Jamhuriyar Benin da Ghana da Sudan da Chadi da Kamaru da sauransu, akwai jama’a da dama da ke amfani da Harshen Hausa. Wannan manuniya ce a kan karɓuwa da faɗaɗa na Harshen a Nahiyar Afirka.

A matakin Duniya kuwa, manyan ƙasashe da waɗanda suke ganin wuyansu ya isa yanka, sun zaɓi su buɗe Tashoshin Rediyo, wasu ma har da na Talabijin don yaɗa shirye-shiryensu a Harshen Hausa. Waɗannan ƙasashe kuwa sun haɗa da Birtaniya da Amurka da Faransa da Jamus da Sin da Farisa da dai sauransu.

Duba da ci gaba da ake ganin Harshen Hausa ya samu, kuma yake kan samu, to a ɗaya hannun kuma, shi ma yana fama da wasu ƙalubale da ya kamata a lura da su, domin kuwa suna cin Harshen, musamman a al’amarin da ya shafi bin ƙa’idojin rubutu a Harshen da ɓacewar tsofaffin kalmomi da rashin killace rubutaccen tarihin da ya dangance shi.

KU KUMA KARANTA: Yau ce ranar Hausa ta duniya

A yanzu, tantance asalin Bahaushe daga waninsa, musamman a Arewacin Nijeriya, aiki ne tuƙuru. Ko da kuwa a jihohi da garuruwa ko anguwanni da ake lissafa cewa mafiya yawa daga mazaunansu Hausawa ne, saboda ana gwamatse da wasu Harsuna, duk da cewa da daman su da Harshen Hausa suke magana. Saboda haka ana samun naso na dabi’a da kuma na magana, domin zamantakewa da cakuɗe da juna da ake da.

Waɗanda asalinsu ba Hausawa ba ne, a lokuta da dama, akan samu wasu kalmomin Hausa da suke ba su wahalar faɗa, sannan wasunsu ma kan karanta Hausa har su zama hujja ko madogara. Sannu a hankali wannan tasirin yana sa hatta Hausawa karɓar yadda waɗanda ba Hausawa suke faɗar wasu kalmomi ko yadda suke fassara wasu abubuwa.

Misali, maimakon a ce “Hira” sai a ce “Fira”. “Gashi” sai a ce “Suya”. “Kai masa”, sai a ce “Kai mai”. “Gona”, sai ace “Gwana”, “Kibiya” sai a ce “Musilla”, “Tsefe gashi”, sai a ce “Kunce gashi ko Since gashi”, “Matata” sai a ce “Matana” da sauransu. Sunayen wasu tsofaffin abubuwa na tarihi da al’ada suna ta ɓacewa. Yara masu tasowa ba lallai su san su ba.

KU KUMA KARANTA: Dalilan da ya sa labaran ƙarya ya fi yaɗuwa – Dakta Hassan Gimba, a hirarsa da RFI Hausa

Misali, yanzu idan ka tambayi ɗan Bahaushe mai shekara 12 ko ƙasa da haka a cikin gari ka ce masa mene ne Shantu ko Zabira ko Gafaka ko Tandu ko Taskira ko Zuga-zugi ko Tsaki da sauransu, sai ya tsaya yana kallon ka. Wasu yanzu ko “Faifai da Akushi da Mara da Kasko da Ƙwarya”, ba su sani ba.

Ba a nan kawai gizo ke saƙa ba, Malaman Hausa da masana Harshen Hausa da dama sun fahimci ci baya da yawa daga Hausawa da masu amfani da Harshen Hausa a rubutu. Ɓarnar da ake yi a rubutu ta yi yawa sosai har daga waɗanda ake ganin ya kamata a ce sun girmi haka ko bai dace a same su da irin waɗannan kurakuran ba, amma abin sai ƙaruwa ya ke yi akai-akai.

A bisa la’akari da yadda muke rubuce-rubuce, musamman a kafafen sadarwa na zamani, na fahimci cewa, Hausawa da waɗanda ke amfani da Harshen Hausa sun fi aikata kurakurai a rubutun Hausa fiye da rubutu cikin Harshen Turanci. Akwai kalmomi da suke haɗe sai a raba su, misali “namu’ da “tamu”, sai ka taras an raba su, kamar haka “na mu” da “ta mu”, da sauransu. Sannan waɗanda suke rabe, sai ka taras an haɗe su, misali “shi ne” sai ka taras an rubuta shi a matsayin “shine” da ire-irensu.

Fahimtar haka, shi ya sa na nemi jin ra’ayoyin mutane da dama a kan dalilan da suka sa Hausawa da yawa ba sa iya rubutu da Hausa tare da kiyaye ka’idojinsa, kuma na sami amsoshi da dama. Alal misali, wasu manazarta na ganin cewa, da yawa suna ganin sun iya Harshen ne a baki, ba su da buƙatar mayar da hankali wajen koyo da kuma bin ƙa’idojin Harshen. Wasu kuma ma ba su san cewa ba su iya rubutun ba. Yayin da wasu masana ke ganin ya kamata a saka Harshen Hausa ya zama wajibi a makarantu, musamman a jihohi da garuruwa na Hausawa.

Ala ayyi halin, lokaci ya yi da hukumomi da masana da ma al’umma gabaɗaya za su dawo cikin taitayinsu domin yi wa wannan Harshe gata wajen ba shi gagarumar gudunmawa domin amfanin kowa da kowa.

Yusuf Alhaji Lawan ya rubuta daga Unguwar Hausawa Asibiti, Potiskum, Jihar Yobe, kuma za a iya tuntuɓarsa a nasidi30@gmail.com.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here