Labarin yana gefen ku!

Hare-haren Amurka da Birtaniya sun kashe mutane da dama a Yemen

1

Amurka da Birtaniya sun kashe aƙalla mutum 11 tare da jikkata 14 a wasu hare-hare da aka kai a yammacin ƙasar Yemen, kamar yadda kakakin gwamnatin da ƙasashen duniya suka amince da shi ya sanar.

An kai hare-hare ta sama aƙalla sau 17 a kasar, ciki har da babban birnin Hudaida mai tashar jiragen ruwa da kuma tashar ruwa ta Ras Isa, a cewar Al Masirah, babbar kafar yaɗa labaran Houthi.

Duk da hare-haren da ƙawancen Amurka da Birtaniya ke kaiwa da kuma na wasu rundunonin sojin ruwa, Houthis sun zafafa kai hare-hare kan jiragen ruwa “mallakar Isra’ila ko mai zuwa Isra’ila” a ɗaya daga cikin manyan hanyoyin jigilar kayayyaki a duniya.

KU KUMA KARANTA: Amurka da Birtaniya sun ƙaddamar da hare-hare kan ‘yan tawayen Houthi na Yemen

‘Yan Houthi sun ce za a ci gaba da kai hare-hare har sai Isra’ila ta dakatar da mamaye da kuma yaƙi a Gaza.

Leave A Reply

Your email address will not be published.