Hadi Sirika Ya Kawo Ci Gaba Ta Fannin Sufurin Jiragen Sama-Inji Na Maroko

0
391

JABIRU A HASSAN Daga Kano.

An bayyana cewa ministan Sufurin Jiragen sama Hadi Sirika ya Kawo ci gaba ta wannan fanni tareda kawo Sauyi a sha’anin hulda da kasashe da Kuma kamfanonin Sufurin Jiragen sama na duniya. 
Wannan tsokaci ya fito ne daga wani fitaccen mawakin siyasa watau Malam Sule Na Maroko Mai Waka cikin wata ganawar su day wakilin mu a Kano, inda kuma ya jaddada cewa Nijeriya tana samun ci gaba mai albarka ta fannin Sufurin Jiragen sama kamar yadda ake gani tun da ya karbi ragamar jagorancin ma’aikatar.
Haka kuma ya sanar da cewa Minista Hadi Sirika yana kishin kasarnan Kwarai da gaske sannan shugaba ne mai kaunar ci gaban wannan kasa duba da yadda yake bada gagarumar gudummawar sa wajen ganin Nijeriya tana bunkasa ta kowane fanni.
Na Maroko mai waka ya kara da cewa ” Ina tare ne da maigirma Minista Hadi  Sirika saboda shi mutum ne jarumi Kuma Wanda yake da bukatar ganin kasar mun ta kasance abar misali cikin sauran kasashen nahiyar Afirka da Kuma duniya ta fuskar Sufurin Jiragen sama, don haka zan ci gaba da kasancewa da shi a tafiya irin ta siyasa”. Inji shi.
Daga karshe, Na Maroko yayi amfani da wannan dama wajen sanar da cewa ya shirya tsaf domin fara bayyana kyawawan nasarorin Minista Hadi Sirika tareda isar da manufofin sa na kyautata zamantakewa da ci gaban kasa ta yadda kowa zai gamsu da salon shugabancin sa.

Hadi Sirika Ya Kawo CI Gaba Ta Fannin Sufurin Jiragen Sama-Inji Na Maroko.

Leave a Reply