Gwanatin Tarayya Ta Jinngine Batun Cire Tallafin Man Fetur

0
383

Gwamnatin Najeriya ta ce za ta ci gaba da bayar da tallafin man fetur a kasar, matakin da ke zuwa a daidai lokacin da ‘yan kasa ke ci gaba da fargaba kan yiwuwar kara farashin mai.

A ranar Litinin ne aka fitar da sanarwa da ke tabbatar da cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta jingine shirin janye tallafin man fetur bayan wani taro da aka gudanar karkashin jagorancin shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmed Lawan.

Mahukunta a Najeriya dai sun yi bayani kan aniyarsu ta ci gaba da ba da tallafin man fetur a wannan shekara wanda tun a farkon wannan shekara ‘yan ƙasar suka shiga fargaba, sakamakon rashin sanya tallafin man fetur a kasafin kuɗin bana.

Mai taimakawa Sanatan kan hulda da jama`a, Alhaji Bashir Hayatu Jantile, ya shaida wa BBC Hausa cewa Sanata Ahmed Lawan ya gayyaci masu ruwa da tsaki kan harkar man fetur inda ya nuna musu damuwarsa da sauran ‘yan majalisar da kuma shaida musu tattaunawar da ya yi da shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar Jantile a wajen taron ne aka samu sabon bayani daga Ministar Kudin Najeriya a kan abin da gwamnatin tarayya ke yi game da batun tallafin man, wanda ake ta rade-radi game da janye shi.

Kuma bayanin da ta yi a gaban shugaban majalisar dattawan, a cewar sa ta kawar da dukkan shakku domin daga na zuwa watan Yuni akwai kudin ci gaba da biyan tallafi, dama matsalar sai daga watan Yuli za ta soma.

Ya ce wannan bayyani ya farantawa sanatocin rai kuma suka yi kira ga kungiyoyin kwadago su tsayar da batun yajin aiki ko bore da suke shirin yiwa gwamnati.

Babu shaka an shiga zaman zulumi a Najeriya game da janye tallafin man fetur.

Tun a karshen shekarar da ta wuce wasu ruwayoyi ke cewa za a janye tallafin, har ta kai ga gidajen mai da dama suka yi ta tsimin man da suke sayarwa a manyan biranen kasar, har da Abuja babban birnin ƙasar.

Wani abin da ya karfafa zaton janye tallafin shi ne rashin sanya tallafin a cikin kasafin kudin kasar na bana.

Ko a lokacin da majalisar koli da ke kula da tattalin arzikin ta yi taro, da dama na yi tsammani za ta fadi ainihin matsayin gwamnati game da janye tallafin. Amma sai ta ce ‘yan majalisar ba su yanke wata shawara a kan wannan maganar ba.

Maganar janye tallafin dai kusan kowa ba ya son alakanta kansa da ita, saboda tana iya janyo bakin-jini.

A dan tsakanin nan ma na ambato minstan man kasar, Timiprye Syva yana cewa shugaban kasar Muhammadu Buhari bai ba da umurnin a janye tallafin man ba.

Masu lura da al’amura dai suna cewa gwamnatin Najeriyar ta samu kan ta a wani yanayi ne na gaba kura, baya sayaki.

Tana son janye tallafin mai, sakamakon kukan rashin kudin da take yi, da zargin cewa wasu kalilan ne ke cin gajiyar tallafin.

Sannan a bangare guda kuma tana gudun bacin ran ‘yan kasar da zai biyo bayan janye tallafin, a wata gabar da ake tunkarar babban zabe.

Leave a Reply