Gwamnatin jihar Zamfara ta bayyana dalilin rufe wasu kasuwannin dabbobi a jihar.
Alfijir labarai ta rawaito a ranar Laraba ne gwamnatin jihar ta sanar da rufe kasuwannin a ƙananan hukumomi bakwai waɗanda ta ce ana hada-hadar shanu da dabbobin sata.
Mannir Haidara Kaura, kwamishinan watsa labarai da raya al’adu na jihar, ya bayyana wa BBC Hausa cewa an ɗauki wannan mataki ne a wani yunƙuri na tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin jama’ar jihar.
Ya ce bayanan da gwamnati da hukumomin tsaro suka samu sun nuna cewa ‘yan fashin daji na shigo da dabbobin da suka ƙwace a hannun mutane suna cinikinsu inda suke samun kuɗin da suke gudanar da harkokinsu na yau da kullum.
KU KUMA KARANTA: ’Yan bindiga a Taraba sun sace mutane ana tsaka da cin kasuwa
Yanayi na tsaro abu ne da ke da sarƙaƙiya, amma dai muna ganin matakan da wannan gwamnati ke ɗauka za su fara tasiri ba da jimawa ba, domin za mu toshe musu wannan kofa” in ji kakakin gwamnatin
Ba dai wannan ne karon farko da gwamnatin jihar ta Zamfara ke rufe kasuwannin dabbobi ba, bisa zargin hada-hadar dabbobin sata da ‘yan fashin daji ke kawowa.
A watan Satumba ma akwai wasu kasuwanni guda bakwai da gwamnatin jihar ta rufe saboda irin wannan zargi, inda ake ci gaba da bincike.
Jihar Zamfara dai na ɗaya daga cikin jihohin da suka fi fama da matsalar tsaro a Najeriya, inda yan fashin daji ke kai hare-hare, suna kashe jama’a da kuma satar dukiyoyinsu, ciki har da dabbobi.
Sai dai gwamnatin jihar na ganin cewa irin waɗannan matakai da take ɗauka, za su taimaka wajen shawo kan matsalar da ta ki ci ta ki cinyewa.