Gwamnatin Matawalle Na Da Alkibla – Dokta Shinkafi

0
410

Daga; MUSTAPHA IMRANA ABDULLAHI.

AN bayyana Gwamnatin Muhammadu Bello Matawalle na Jihara Zamfara da cewa gwamnati ce mai Alkibla da kowa ya san inda ta dosa a duk fadin duniya baki daya.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi, Mai ba Gwamnan Jihar Zamfara shawara a kan hulda da kasashen waje da kuma yin yarjejeniya ya bayyana hakan a cikin wata takardar da aka rabawa manema labarai.

Dokta Suleiman Shu’aibu Shinkafi ya ci gaba da bayanin cewa hakika duk wanda ya yi za a yi masa a Gwamnatin Dokta Bello Matawalle.

A halin yanzu an Sanya kwamiti kuma ” an cire Sarkin Dan Sadau da Zurmi”.

Hakika ya tabbata cewa Gwamnati ce da ke kokarin kwatowa talakawa hakki, saboda hakan ya nuna cewa Gwamnan, Mataimakinsa da sauran mukarrabansa duk su na da Alkibla, ba jeka na yi ka ba”, inji Dokta Shinkafi

Saboda haka, yanzu muka dora tubalin yin tafiya mai kyau a Jihar Zamfara domin kamar yadda kowa ya sani an dora tubalin yin tafiya ta musamman a Jihar Zamfara.

“Ina tabbatar maka daga nan zuwa dan kankanin lokaci, Talakan Zamfara zai warke zai samu sauki da dukkan sa’idar da ya dace ya samu a game da abubuwan da ke faruwa, hakan ya sa muke yin kira ga talakawan Jihar Zamfara da su godewa Allah da ya ba su wannan Bawan Allah, saboda haka ne muke yi wa dukkan talakawan Jihar Zamfara albishir da cewa a yanzu Gwamnatin nan ta Daura aniyar ceton Talakawa baki daya domin fitar da duk wani kunci tare da Daura aniyar yaki da duk wani mutum da ba zai bari a zauna lafiya ba daman kamar yadda karin magana yake ne duk dan da ya hana uwarsa Bacci shi ma ba zai runtsa ba don haka ga Dodo nan ga su” , inji Dokta Suleiman Shinkafi.

Leave a Reply