Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
GWAMNATIN Jihar Kaduna ta tabbatar da kisan wasu mutane talatin da biyu (32) a ciki wani sabon harin da wasu yan Bindiga suka kai a cikin yan kwanakin nan a wasu kauyukan da ke karkashin karamar hukumar Kajuru ta Jihar Kaduna, kana ta karyata wani bayanin da ke cewa ‘yan Bindigan sun koma kai hari a wani Jirgi mai saukar Ungulu.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takarar sanarwa da kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Samuel Aruwan ya fitar a ranar Alhamis.
Sanarwar ta kara da cewa, “ta samu rahoton farko daga hukumomin tsaro, cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyukan Dogon Noma, Unguwan Sarki da Unguwan Maikori a karamar hukumar Kajuru a ranar Lahadin da ta gabata.”
Rahotanni sun bayyana cewa, ‘yan bindigar sun mamaye yankin a kan babura inda suka yi ta lalata gidaje da dama, yayin da suka kai hari tare da kashe wasu mutanen yankin.
Acewarta, tun bayan harin da aka kai a ranar lahadi, hukumomin tsaro da shugabannin gargajiya da ke wuraren ke ta kokarin tattara bayanai game da ci gaban da ake samu kana suke sanar da Gwamnatin.
Sanarwar ta ce, ya zuwa lokacin wannan rahoto, an tabbatar da mutuwar mutane 32 bayan harin.
Yayin da Gwamnati ke jimamin kisan gilla da kona gidaje da aka yi a wuraren da aka kai harin, an buga wani rahoto da ke nuni da cewa ‘yan ta’adda sun kashe wadanda harin ya rutsa da su ta hanyar amfani da jirgin sama mai saukar ungulu.
Gwamnatin Jihar Kaduna na son yin karin haske kan rahotannin da aka samu tun ranar Lahadi, inda ta ce ‘Yan bindigar sun kai hari a wurare biyu a yankin, na farko inda suka kashe mutane 31 a yankin, kana daga nan suka nufi Ungwan Maikori, inda suka kashe mutum daya tare da kona wasu gidaje.
“Tun da farko, wani jirgin sama mai saukar ungulu (a karkashin Operation Whirl Punch) ya kai shawagi na agaji a yankin inda ya leka wurare biyu, kuma wuri na farko, ya kuma hango kone-konen gidaje da kadarori.
“Jirgin sama mai saukar ungulu ya tare ‘yan bindigar a wasu wurare yayin da a wuri na karshe (Ungwan Maikori) ya samu nasarar tare su har da kama su yayin da suke kokarin tsere wa, kafin isowar sojojin kasa izuwa yankin gaba daya don kai agaji.
Ta ce “Isowar dakarorin jirgin ne ya hana ‘yan bindigar ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan kauyen bayan ‘yan bindigar sun kashe wani dan unguwar tare da kona gidaje da dama.
“Labarin cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu ya bayar da tallafin sama ga ‘yan bindigar kan mutanen yankin, wannan labarin ba gaskiya ba ne, don haka magana ce mara tushe.
“Gwamnatin jihar Kaduna da ta bi diddigin al’amura, ta ga abin takaicin yadda wani sashe na kafafen yada labarai ke yada wani rahoto da ba a tabbatar da shi ba, ba tare da la’akari da tasirinsa kan tsaro, doka da oda ba.
“An gayyaci shaidun gani da ido kan rahoton wani jirgin sama mai saukar ungulu da ke taimaka wa ‘yan bindiga da ke kashe mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, da su gabatar da bayanan ga gwamnati bisa goyon bayan hujjojin da ba za a iya tantancewa ba.
“Sojoji, ’yan sanda da sauran hukumomin da ke aiki a yankin gaba daya sun cancanci yabo da kwarin gwiwa ne, maimakon rage musu kwarin gwiwa.
“A cikin sa’o’i 72 da suka gabata, jami’an tsaro sun gudanar da wani gagarumin farmaki a yankin gaba daya, kuma suna kan bin wani fitaccen dan ta’adda da ya jikkata.
“Hakazalika, wasu da dama da aka yi garkuwa da su, ciki har da wani dan kasar waje da aka yi garkuwa da su a wani wurin hakar ma’adinai, an kubutar da su bayan mumunar hulda da ‘yan fashi.
“Gwamna Nasir El-Rufa’i da ya samu rahoton harin, ya nuna matukar bakin ciki tare da addu’ar Allah ya jikan wadanda lamarin ya shafa. Ya kuma mika sakon ta’aziyyarsa ga iyalan wadanda lamarin ya shafa,” in ji sanarwar.
[…] KU KUMA KARANTA:Gwamnatin Jihar Kaduna Ta Tabbatar Da Kisan Mutane 32, Yayin Da Ta Karyata Zancen Jirgi Mai Saukar U… […]