Gwamna Buni ya ba da tallafin karatu ga ɗaliban koyon Shari’a kimanin 221 a Yobe

0
189

Daga Sani Gazas Chinade, Damaturu

Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya ba da tallafin karatu ga ɗalibai 221 da suka kammala karatu a fannin shari’a daga Jami’o’i daban-daban a faɗin ƙasar nan a wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa ilimi.

Wannan taron ba da tallafin ya gudana ne a babban  ɗakin taro na Banquet da ke gidan gwamnati da ke Damaturu, wanda ya samu halartar manyan baƙi daga kowane lungu da saƙo na jihar.

A nasa jawabin, gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni ya taya waɗanda suka ci gajiyar tallafin murna “bari in fara da taya ku murnar kammala karatun digiri a fannin shari’a a jihar Yobe tare da yi muku fatan alheri a lokacin da kuke shirin neman takardar shedar ƙwarewa a babbar Makarantar koyar da shari’a ta ƙasa (Nigerian Law School).

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya nemi haɗin kan jami’o’in Burtaniya uku, don bunƙasa harkar ilimi a jihar Yobe

Ya bayyana cewa, “Kamar yadda kuka sani, wannan gwamnatin ta ba da fifiko ga samar da ingantaccen ilimi tun daga tushe ta hanyar manyan makarantu, da kwasa-kwasa kamar fannin shari’a, fannin lissafi da kudaden, fannin koyon Likitanci da sauransu.”

“Wannan shi ne dalilin da ya sa gwamnatinmu ta tsaya tsayin daka wajen samar da yanayi mai kyau a makarantunmu ta hanyar sake gina makarantun da suka lalace  da kuma kafa sababbi.”

“Mun kuma ba da kayan koyo da  koyarwa ga manyan makarantunmu da cibiyoyin kiwon lafiya da su ma muke ƙoƙarin wadata su da kayan kiwon lafiya.”

“Na yi farin cikin bayyana irin  gamsuwa ta bisa ƙoƙarin wannan gwamnati na samun  daidaiton wajen inganta fannin ilimi ya kasance mai amfani kamar yadda aka nuna a irin hazaƙar dalibanmu gaba daya.”

“Abin farin ciki ne cewa jihar Yobe ta ci gaba da zama ta ɗaya da ba a doke ta ba a shiyyar Arewa maso Gabas, da kuma a cikin jihohin Nijeriya, inda Makarantar koyon shari’ar ta ba wa ɗalibanmu wannan damar don neman takardar shedar ƙwarewa cikin sauƙi.

“Ina so in tabbatar muku da cewa wannan gwamnatin za ta ci gaba da yin tsayin daka wajen bayar da guraben karatu ga ‘yan asalin Yobe da suka cancanta a manyan makarantu a gida da kuma cibiyoyin karatu a ƙasashen waje a faɗin duniya”.

Ya ƙara da cewa, “bikin bayar da tallafin karatu ga ɗaliban mu na Lauyoyin da za su halarci makarantar koyon aikin lauya ta Najeriya ya taimaka wa wannan gwamnati a cikin shekaru huɗun da suka gabata ga ɗaliban da ke karatun lauya ta wajen samun shaidar ƙwarewa a wannan fanni  ya yi dai-dai da tsarin da muke da shi na ci gaban ilimi ”.

“Saboda haka, ya kamata ku bi kwas ɗin ku na ƙwararru tare da sa  himma don mayar da jiharmu abin alfahari a kan wannan fanni na shari’a.”

“Ya kamata ku yi ƙoƙari ku zama jakadu nagari na jihar, kuma ku ci gaba da kasancewa wuraren nunin ƙwararrun ilimi da ɗabi’a.”

“Bari na kuma tabbatar muku da cewa gwamnati za ta sa ido sosai kan ayyukanku a yayin gudanar da karatun ku tare da ba ku tallafin da ya dace don samun nasara.

“Ina yi muku fatan samun nasara sosai kuma ina fatan halartar bikin yayewar ku a karshen karatun ku, kuma ina muku fatan alheri.” 

Leave a Reply