Gobara ta halaka wani yaro ɗan shekara 4 a Kano

0
84

Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano ta tabbatar da mutuwar wani yaro mai kimanin shekara huɗu mai suna Abubakar Sani, sakamakon gobarar da ta tashi a Yakasai, Layin Inuwa mai mai a Ƙaramar Hukumar Birnin Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Alhaji Saminu Abdullahi ne ya bayyana hakan a Kano.

Saminu ya bayyana cewa, hukumar ta samu ƙiran gaggawa daga ma’aikacinsu Habibi Adamu game da gobarar a Yakasai.

Ya kuma yi nuni da cewa, nan take aka hada tawagar ceto daga ofishin hukumar kashe gobara da ke Sakatariyar Audu Bako a birnin Kano.

Jami’in hulɗa da jama’a ya yi nuni da cewa, ginin bene daya mai tsawon mita 40 da 30 da ake amfani da shi a matsayin gidan zama, daƙi ɗaya da ke benen ne ya ƙone gaba ɗaya sakamakon gobarar, yayin da falo ɗaya ya ƙone kaɗan.

KU KUMA KARANTA: Gobarar daji ta halaka mutane sama da 51 a Chile

Ya ce, yaron ya maƙale a ɗakin da wutar ta kama har ta cinye shi. Kuma duk ƙoƙarin da aka yi na ceto shi kafin isowar ‘yan kwanakwana ya ci tura.

Saminu ya ci gaba da cewa, an ceto wanda abin ya shafa a sume kuma aka kai shi asibitin ƙwararru na Murtala Muhammed, inda likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da rasuwarsa.

Ya ce, gobarar ta tashi ne sakamakon yadda yaron da abin ya shafa ke wasa da ashana a cikin ɗaki.

Saminu ya buƙaci iyaye da su daina jefa ’ya’yansu cikin hadari ta hanyar barin su ba tare da kula da su ba da kuma nisanta su da abubuwa masu hatsari.

Leave a Reply