Flora Nwapa, jagorar mata adabin zamani na Afirka

1
330

Ƴar Najeriya mawallafiya Flora Nwapa, littafinta Efuru ya sa ta zama mace ta farko da ta wallafa littafi da turanci.

Aikinta ya share fage ga bayyanar mata mawallafa a Najeriya da sauran ƙasashen Afirka. An haifi Flora Nwapa a watan Janairu na shekarar Alif da Ɗari Tara da Talatin da Ɗaya (1931), a Oguta, jihar Imo, a Gabashin Najeriya.

Ta fara karatunta a Oguta da Fatakwal da kuma Legas. Ta yi makarantar kwalejin jami’ar Ibadan a Najeriya da jami’ar Edinburgh a Birtaniya. Nwapa ta rasu a watan Oktoba, Alif da Ɗari Tara da Casa’in da Uku (1993), sakamakon ciwon pneumonia (nimoniya) ta na da shekaru Sittin da Biyu.

Ta hanyar littattafanta, Flora Nwapata, ta yi ƙoƙarin sauya labaran maza marubuta na Afirka waɗanda rubuce-rubucensu ke cike da saɓanin tunani kan matan Afirka. Littattafan Nwapa sun bayyanar da akasin haka, inda ta riƙa ba da labarai na nasarori da matan Afirka suka samu.

Littattafanta kamar Efuru da Idu sun ƙalubalanci al’adar yadda ake bayyana matan Afirka a matsayin waɗanda dole a ko da yaushe su kasance ƙarƙashin inuwar maza saboda ana ɗaukar mace a matsayin ya kamata ta bi, ta miƙa wuya kuma wacce ba ta da wani amfani.

Ɗaya daga cikin littattafan Flora Nwapa, da suka shahara shi ne Efuru. Littafin ya bayyana rayuwar wata mata wacce ta nuna ƙarfin hali da ƙarfin zuciya har ma da taimaka wa mijinta da mahaifinta da kuɗaɗe.

Efuru, tauraron labarin littafin ya sauya tunanin mayar da mata baya da ake nunawa a zamantakewar al’adar gargajiya ta al’ummar Afrika, inda ta nuna nata ra’ayin na dabam.

Ta zartar da wasu ƙudurori muhimmai a rayuwarta bisa abin da take gani ya dace da ita maimakon miƙa wuya ga buƙatun al’adun gargajiya na Afirka. Sauran littattafai da ta wallafa sun haɗa da: Idu da Never Again da One Is Enough da kuma Women Are Different.

Babban abin da za a tuna ta da shi, shi ne samar da mata marubuta waɗanda suke maimaita jigon littattafanta a wani yunƙuri na sauya labarai marasa daɗi game da matan Afirka a yanayin da maza suka kankane fagen adabi.

Yayin da Flora Nwapa ba ta ɗaukar kanta a matsayin mai gwarwarmayar daidaiton jinsi, wasu daga cikin littattafanta sun shahara wajen kare hakkin mata. A rubuce-rubucenta ta na amfani da sunayen mata wajen ƙalubalantar al’adu na rashin adalci ga mata wanda har yanzu yake ƙarfafa guiwar mata ƴan fafutuka.

1 COMMENT

Leave a Reply