CIBN, Za Ta Ci Gaba Da Samar Da Tallafi Domin Samun Kwarewa A Harkar Aikin Banki – Wada Nas

0
356

JABIRU A HASSAN, Daga Kano.

WANI Jami’in cibiyar Koyar da kwarewa kan aikin banki na jihar Kano watau ” Chartered Institute Of Banking Of Nigeria” (CIBN), Alhaji Aliyu wada Nas ya jaddada cewa yadda cibiyar ke samar da yanayin koyo da koyarwa kan aikin banki za a ci gaba da samun kwararru a wannan fanni a fadin wannan kasa.

Ya yi wannan albishir ne yayin da ya zanta da manema labarai wajen bikin aza harsashin ginin wani katafaren dakin Daukar Darasi wanda zai dauki dalubai 160, inda ya bayyana cewa samar da kyawawan guraren daukar darussa zai taimaka wajen samun karatu ingantacce tare da samar da kwararru kan sha’anin aikin banki.

Sannan ya nunar da cewa cibiyar su ta CIBN tana gudanar da abubuwa muhimmai wadanda zasu taimaka wajen samar da yanayi mai gamsarwa ta fuskar harkokin banki da samun kwarewa kan aiwatar da dukkanin wasu manufofi da suka shafi aikin banki da sauran fannoni da suka shafi hadahadar kudade.

A karshe Aliyu wada Nas ya bukaci daluban wannan makaranta zasu yi amfani da dakin daukar karatun yadda ake bukata ta yadda zau ci gajiyar aikin, tareda sanar da cewa da yardar Allah, za’a kammala ginin cikin makonni 6 domin fara amfani da shi.

Leave a Reply