Buni Ne Gwarzon Jaridar Authentic Na Shekarar 2021, Nimrod Ya Ci Nasarar Ƙimar Wasanni Sau 4

0
607

Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.

BABBAN shafin yada labarai na yanar gizo da ke Kaduna, Authentic News daily ya sanar da wadanda suka lashe kyautar babbar lamba yabo bugu na bakwai na shekara ta 2021.

A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Editan ta, Okpani Jacob Onjewu Dickson, wanda aka bayar a ranar Lahadi 2 ga watan Janairu, 2022 ta sanar da cewa Gwamnan Jihar Yobe kuma Shugaban Kwamitin Riko na Jam’iyyar APC mai mulki, Malam Mai Mala Buni ne ya zama Gwarzon da ya yi nasara a shekarar ta 2021.

Hakazalika, an sanar da cewa zababben gwamnan Jihar Anambra, Charles Soludo, shi ne Ingantaccen dan Siyasa na shekarar 2021 da shafin yanar gizo ta karrama.

Fitacciyar ‘yar fafutuka, Aisha Yesufu ta zama gwarzuwar mace ta bana, yayin da Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya ya zama gwarzon dan wasan na bana, kana shi ne ya zama wanda ya lashe lambar yabon a karo na hudu, bayan da ya lashe haka a 2017, 2019 da 2020.

“Kamar yadda aka yi a cikin bugu na shida da suka gabata, wadanda suka lashe kyaututtuka a cikin nau’ikan 17 sun fito,” in ji shi.

Sanarwar ta taya wadanda suka samu nasara murna, yayin da ta bukace su da su ci gaba da gudanar da ayyukan alheri da ya sa aka karrama su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here