Wannan birni ya sanya Masar a matsayi na shida a duniya wajen samar da Mangwaro tan miliyan biyu a duk shekara, bayan ƙasashen Indiya, Sin, Thailand, Mexico da Indonesiya.
Birnin Ismailia, ya na samar da nau’ikan Mangwaro daban-daban sama da kala talatin da suka shahara da kuma inganci.
Ismailia, ya na gaɓar yamma da tashar ruwa na Suez Canal. Ana ɗaukarsa a matsayin ɗaya daga cikin mafi kyawun birane masu ƙayatarwa a Masar, tare da tsaftatattun tituna da tsirrai, da kuma manyan lambuna.
Birnin shi ne babban yankin da ake noman Mangwaro a ƙasar, wadda ya shahara wajen samar da Mangwaro masu inganci saboda ƙasa mai kyau da yanayi. Girbin Mangwaro ya na farawa a ƙarshen watan Yuli kuma ya na ci gaba har zuwa ƙarshen Satumba.
Sauran amfanin gona da ake nomawa a yankin sun haɗa da; Strawberry, Lemu, Zaitun, Inibi, Gyaɗa, da sauransu.
KU KUMA KARANTA:Burin Turkiyya shi ne samun cikakken ƴanci a ɓangaren makamashi – Shugaba Erdogan
A shekarar da ta gabata ne (2023), birnin ya fara shirya bikin Mangwaro na farko a ƙasar, inda jakadun New Zealand, Indonesia, Philippines, Saudi Arabia, Najeriya, Jordan da Sri Lanka duk sun halarci buɗe taron.
Masu shirya taron sun ce, maƙasudin taron shi ne, bunƙasa Mangoron Masar don fitar da su zuwa ƙasashen waje da kuma samar da sabbin masu zuba jari da guraben ayyukan yi a fannin, tare da ƙarfafa harkokin yawon buɗe ido a lardin Ismailia.
Hukumomin yankin sun bayyana cewa, birnin na noma kashi ɗaya bisa uku na Mangwaron da ake nomawa a ƙasar, inda ake noma sama da kadada 35,612ha.
Har ila yau, ana fitar da Mangwaro da sauran amfanin gona da suka kai dalar Amurka biliyan 1.4 cikin shekaru uku da suka gabata.