Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
BABBAN mai kula da cocin Christian Evangelical and life intervention Church, Fasto Yohanna Buru, ya rabawa yaran musulmai marayu da wasu matan da mazajensu suka rasu Kayayyakin tallafi domin bukukuwan sallah.
A cewarsa, ya yi hakan ne da zummar tallafa wa marayu hamsin ne domin su samu damar gudanar da bukukuwan Sallah cikin farin ciki da jin dadi kamar yadda sauran yara ke gudanar da bukukuwan.
Fasto yohanna ya ce wannan ba shi ne karon farko da cocin ke raba sabbin tufafi da kayan abinci ga marayu da matan musulmi zawarawan da suka rasa mazajensu, domin karfafa hadin kan addinai da kuma nuna zaman lafiya a tsakanin kungiyoyin addinai daban-daban a kasar.
Manufar ita ce tabbatar da dangantakar Kirista da Musulmi a kasar, da samar da zaman lafiya, hadin kai, yafiya a tsakanin mabiya addinan biyu.
Limamin na Kirista ya taya al’ummar Musulmi a fadin duniya murnar kammala azumi na kwanaki 30 cikin nasara.
(Majami’a ba za ta manta da gudunmawar shekara-shekara da wata mata musulma hajiya Ramatu Tijjani ta bayar na tunawa da zawarawa da marayu na cocin da kayan abinci da kuma kyautar Kirsimeti ga Fasto da sauran Rabaran).
(A shekarar da ta gabata Ramatu Tijjani tana raba kayan abinci na Kirsimeti da sauran kyaututtuka ga ’yan coci)
Buru ya ce, za su kara raba tufafi ga marayu marasa galihu domin gudanar da wannan Sallah cikin farin ciki kamar kowane yaro.
Bikin Sallah na bana ya zo ne a daidai lokacin da ake samun karuwar kayan abinci a kasuwanni da kuma kalubalen rashin tsaro na rashin zaman lafiya a kasar.
Yayin da yake kira ga malaman addinin Musulunci da na Kirista da su kara kaimi wajen gudanar da addu’o’in neman zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasar
Ya taya mai alfarma Sarkin Musulmi, alhaji Abubakar Sa’ad, Sheikh Zazzaky Yakub El-zakzaky, Sheikh Dahiru Bauchi, Sheikh Hamza lawal da kuma Sheikh Dakta Ahmed Mahmud Gumi da sauran manyan malaman addinin musulunci murnar kammala Azumin watan Ramadan.
Buru ya ce, za su kai ziyarar sada zumunci a lokutan bukukuwan Sallah ga takwarorinsu na Musulmi domin bunkasa alaka tsakanin Kirista da Musulmi a kasar.
Da yake mayar da martani, daya daga cikin marayun da suka samu tallafin ya godewa Fasto yohanna buru bisa tunawa da su.
Ya ce ko a bara ma faston ne ya ba shi sabbin tufafin Sallah da ‘yan kudi na bikin Sallah.
Ya kuma yi kira ga Gwamnati da ta rika tunawa da marayu da yara a wuraren da ke gidajen yan Gudun Hijira.
[…] KU KUMA KARANTA:Bikin Sallah: Wata Cocin Kaduna Ta Raba kayan sawa, Kayan abinci Da Tsabar Kudi Ga Marayu Sama Da 50 […]
[…] KU KUMA KARANTA: Bikin Sallah: Wata Cocin Kaduna Ta Raba kayan sawa, Kayan abinci Da Tsabar Kudi Ga Marayu Sama Da 50 […]