Labarin yana gefen ku!

Basaraken da ake nema game da kisan sojoji ya miƙa kansa

3

Ƙasa da awa 24 bayan fitar da sanarwar da hedikwatar tsaron Najeriya ta yi, Basaraken, Clement Ikolo ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar Delta inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.

Rundunar ‘yansandan jihar Delta a kudu maso kudancin Najeriya ta ce Sarkin Masarautar Ewu a jihar Delta, Clement Ikolo ya miƙa kansa ga rundunar a ranar Alhamis.

Ikolo wanda Basarake ne a ƙaramar hukumar Ughelli a jihar ta Delta, na ɗaya daga cikin mutum takwas da Hedikwatar Tsaron Najeriya ta fitar da sanarwar tana neman su ruwa a jallo.

Mutanen sun haɗa da Farfesa. Ekpekpo Arthur, Andaowei Dennis Bakriri, Akevwru Daniel Omotegbo (Aka Amagben), Akata Malawa David, Sinclear Oliki; Clement Ikolo Oghenerukeywe; Reuben Baru da Igoli Ebi.

“Hotunan mutanen da ake nema game da hannu a kisan sojojin Najeriya 17 a Ukuama da ke ƙaramar hukumar Ugheli ta kudu a jihar Delta a ranar 14 ga watan Maris.” Sanarwar da hedkwatar tsaron Najeriyar ta wallafa a ranar Alhamis a shafinta na Facebook ta ce, haɗe da hotunansu.

KU KUMA KARANTA:Kotun ICJ ta umarci Isra’ila da ta ɗauki matakan magance yunwar da ake fama da ita a Gaza

Daga cikin mutanen akwai maza bakwai da mace ɗaya.

Sai dai ƙasa da sa’a 24 basarake Ikolo ya miƙa kansa ga rundunar ‘yan sandan jihar.

Gidan talbijin ɗin Channels ya ruwato cewa da misalin ƙarfe 6:41 na yamma Basaraken ya kai kansa ga ‘yan sandan.

Jaridar Leadership ta ce Ikolo ya gana da manema labarai gabanin miƙa kansa inda ya ce ba shi da hannu a kisan sojojin.

A ranar 14 ga watan Maris wasu matasa suka halaka sojojin Najeriya 17 cikinsu har da manyan ofisoshi hudu a yankin Ukuama a jihar ta Delta.

Leave A Reply

Your email address will not be published.