Labarin yana gefen ku!

Babu ɗalibin da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi a mulkina – Tinubu

1

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya lashi takobin cewa a mulkinsa, babu ɗalibin da zai bar makaranta bai kammala ba saboda kawai ba zai iya biyan kudin makaranta ba.

Ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a bikin yaye ɗalibai karo na 33 da Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Akure a Jihar Ondo ta shirya ranar Asabar.

Tinubu, wanda tsohon shugaban Kwalejin Lafiya ta Afirka ta Yamma, Farfesa King-David Terna Yawe, ya wakilta, ya buƙaci ƙungiyoyi daban-daban na manyan makarantu da su haɗa kai da gwamnati domin tabbatar da zaman lafiya a cikin makarantun.

Game da shirin gwamnatinsa na ba ɗalibai rance kuwa, Tinubu ya ce, “Wannan shiri zai ba dukkan ɗalibai masu ƙaramin karfi damar karɓar bashi mara ruwa, wanda za su iya biya daga baya, idan suka fara aiki.

KU KUMA KARANTA: Gwamna Buni ya nemi haɗin kan jami’o’in Burtaniya uku, don bunƙasa harkar ilimi a jihar Yobe

“Matukar ina mulki, kamar yadda na faɗa a ƙundin manufofina, babu wani ɗalibi da zai bar makaranta saboda rashin kuɗi.

“Gwamnatina ba za ta yi wasa da nauyin da ya rataya a wuyanta ba a wannan bangaren. Za mu tabbatar dukkan manyan makarantu sun sami kudadensu saboda su yi ayyukansu yadda ya kamata,” in ji Tinubu.

Sai dai Shugaban ya shawarci ƙungiyoyin ma’aikatan manyan makarantu da su rungumi hanyoyin tattaunawa na ruwan sanyi a maimakon a kodayaushe su riƙa tsunduma yajin aiki, matakin da ya ce yana gurgunta tsarin ilimi a ƙasar nan.

Leave A Reply

Your email address will not be published.