Ba za mu yi sulhu da Ethiopia ba sai ta soke yarjejeniyar da ta ƙulla da yankin Somaliland — Somaliya

Somaliya ta ce ba za ta yi sulhu da Ethiopia ba sai birnin Addis Ababa ya soke yarjejeniya mai cike da ce-ce-ku-ce ta yin amfani da tashar jiragen ruwa da ya ƙulla da yankin Somaliland da ya ɓalle daga ƙasar.

“Ba za mu buɗe wata kofa ta sulhu da Habasha ba sai ta janye daga haramtacciyar yarjejeniyar sannan ta amince da ‘yancin Somalia na kasancewa ƙasa mai gashin kanta,” in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Somalia a wani sako da ta wallafa a soshiyal midiya ranar Alhamis.

Ƙasashen biyu sun daɗe suna rigima kan batun iyakoki, inda suka yi yaƙi sau biyu a ƙarshen ƙarni na 20.

Ranar Alhamis gwamnatin Somaliland ta yi zargin cewa da gangan Somalia “ta karya alƙawurran da ta yi a baya da Somaliland” ciki har da batun tsaro da amfani da sararin samaniya.

KU KUMA KARANTA: Somaliya ta shiga ƙungiyar ƙasashen gabashin Afirka

Ta yi zargin ne bayan Hukumar Kula Da Sararin Samaniyar Somaliya ta ce ta hana jirgin saman Ethiopian Airlines sauka a Hargeisa, babbar birnin Somaliland ranar Laraba.

Kazalika ranar Alhamis, hukumar ta hana wani jirgin ɗaukar kaya da aka yi wa rajista a Thailand shiga sararin samaniyar Somaliya domin isa Hargeisa daga birnin Sharjah na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa.

Kwamitin Sulhu na Ƙungiyar Tarayyar Afirka ranar Laraba ta yi ƙira ga makwabtan biyu su “yi taka-tsantsan, su daina tayar da jijiyoyin wuya sanna su yi tattaunawar da za ta wanzar da zaman lafiya”.


Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *