Anfanin Ayaba a Jikin Ɗan’Adam

0
614

1)Ayaba takan taimaka yadda ciki zai sami sauqi wajen narka abin da aka ci, sabid ta ƙunshi Starch wadda ake samu a cikin Carbohydrates.
Ba shakka yakan taimaka wajen rage ƙiba, ta yadda jiki zai fara ɗiban wannan starch ɗin a hankali, sannan mutum zai riƙa jin cewa ya ƙoshi, sai ya rage cin abincin dayawa.

2) Ayaba takan sassautar da hauhawar jini, don tana da Potassium, shi kuwa yana da mahimmanci wajen wannan aikin.

3) Zai yi kyau mutum ya sanya Ayaba a matsayin ɗan abin da zai riqa jefawa a baki lokaci zuwa lokaci kafin cin abinci, domin tanasa ƙoshi. Ya fi mutum ya ci abin da zai ƙara masa ƙiba.

  1. 4). Idan mutum ya ji wata ‘yar kasala sai ya janyo guda yaci ta a baki, yafi mai lafiya da sa kuzari akan wasu juice ɗin da suke dauke da Caffeine. Abin birgewa shine yadda ba ta da sukari sosai don dacewa da ci lokaci-lokaci, kamar in mutum yana wajen aiki, ko tarurrukan da kan ɗauki dogon lokaci, ko ma kallon talabijin.
  2. 5.) Ayaba takan kusan zama wajibi ko don lafiyar hanji, Ayaba ƙwara ɗaya tal za ta iya yi wa mutum maganin basir, don tana da wani nau’in Fibres na masamman wanda yake taimaka wa hanji wurin aikinsa, wannan magani halittacce ya fi ƙara lafiya sama da magungunan kampani, masamman tunda suna da illa.

6). Banda wannan kuma Ayaba takan sanya kwanciyar hankali da dadin rai, domin tana da sinadarin Tryptophane wanda ɗaya ne daga cikin sinadarorin da suke natsar da mutum da ba shi kwanciyar hankali na haƙiƙa, ta daidaita tsarin Protein a jiki, don ba wa mutum cikakkiyar sakewa.

7). Da a a ce mutum zai rinƙa cin Ayaba sau uku a rana, wato wajen kari da wurin kalacin rana ko na maraice, to Potassium ɗin dake cikinta zai ƙarfafa ƙwaƙwalwarsa. Wannan yana da mahimmanci ga ɗalibai don yakan ƙara musu nutsuwa da fahimta sosai a lokacin ɗaukar darasi.

8.) Game da mata masu ciki kuwa Ayabar takan taimaka don tana da fa’ida ba ƙarama ba ga mai juna biyu, masamman lokacin da take jin laulayi ko tashin zuciya wanda yake yawan faruwa idan cikin yana ƙarami. Sannan Ayabar za ta iya taimaka musu wajen ganin Glucose dake cikin jininsu bai nemi qaruwa ba, takan kuma lura da yanayin zafin jiki.

9) Sai kuma zancen cizon sauro, wani in sauro ya cije shi sai ka ga wurin ya yi hulu-hulu, to a irin wannan yanayin za a iya bare Ayaba a sanya bawon a wurin, don yakan magance qaiqayin da wurin yakan yi, shi ma wannan ya fi aminci sama da magungunan da mutum zai yi tashafawa.

10). Ayaba takan taimaka kuma wajen magance Ulcer, ko kuma riga-kafin hakan, domin tana ƙanƙanta acid ɗin da abinci yakan bari a tumbi, tawajen daidaita acids din, tareda narka abincin, da wannan sai ka ga ta yi maganin matsalolin tumbi da dama.

11). Ayaba tana da Iron sosai da gaske ga wadan da suke da cutar fatarar jini ko Anaemia, don Iron ɗin kan taimaka masamman ga ƙwayoyin jan jini wanda yake kula da ɗauko Oxygen, ya kuma tabbatar da cewa ruwan jiki wato white blood ya ba da gudummuwarsa wajen magance raunuka.

12) Wani abin mamaki ayaba hatta a gona ɓawonta yana da amfani, don kuwa takan zama taki idan aka kai ta can, kenan a maimakon a riƙa zubarwa gwara a kai shi can inda za a yi aiki da shi don abincin da za mu ci.

13). Ayaba takan taimaka sosai wajen kiyaye lafiyar ƙoda, ta yadda take ƙanƙanta tura Calcium zuwa fitsari, da ƙaranta yuwuwar kamuwa da tsakuwar ƙoda, kamar yadda bincike ya gano cewa cin ayaba yakan rage hatsarin kamuwa da kansar ƙoda, ta yadda aka sami mata waɗan da suke cin ayaba sau 4-6 a sati yadda suka nesanta da kamuwa da kansar qoda sama da wadan da ba sa ci, ban da wannan ma sinadarori masu dama da suke cikin ayaba sun sanya tana iya kawar da matsalar Ulcer kai tsaye.

14.) Galibin Ayaba har da karkasuwar nau’o’inta duk tana dauke da sinadarori kala daban-daban, akwai ma doguwar Ayaba wace yawancinta Inyamurai muke ganin suna sayar da ita, ba a iya cinta sai an soya, ko kuma a gasa ta a wuta, mukan ga ana sanya ta ne a abinci kamar shinkafa, sai a yanyanka ta a dora ta a sama, sunanta Plantain, sukan kira ta da Larabci “Mauzul Janna” ita wannan Ayaba tana da starch sosan gaske, kuma ba ta da sukari mai dama, ita ma tana da tasiri wajen kawar da maiqo a cikin jini, a taqaice dai ita ma ayaba ce.

Leave a Reply