An ɗauko gawar mutum biyu da gini ya danne a Legas

0
516

An zaƙulo gawar mutum biyu daga cikin shida da ɓaraguzan gini suka danne bayan wani bene mai hawa bakwai ya rikito a birnin Legas da ke kudancin Najeriya.

Wani gini mai hawa bakwai da ba a kammala ba ya rushe a birnin Legas, inda ya ritsa da mutane da dama. Rahotanni na cewa ginin, wanda ke kan Titin Oba Idowu Oniru, ya ritsa da mutum kusan shida bayan faɗowarsa a cikin dare wayewar garin Lahadi.

Sakataren hukumar agajin gaggawa reshen Jihar Legas, Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce tuni suka ƙaddamar da aikin ceton waɗanda ginin ya rufe.”Zuwanmu wurin ke da wuya muka tarar ginin mai hawa bakwai da ba a kammala ba ya rikito,” a cewarsa. “Babu rahoton ko wani ya ji rauni amma ana zaton ɓaraguzai sun rufe mutum shida.”

Ya ƙara da cewa ma’aikatansu na buƙatar “manyan kayan aiki” a yunƙurin ceto mutanen, yana mai cewa sun ƙaddamar da “shirin aikin ceto na gaggawa na Jihar Legas”. A makon da ya gabata ma wani gini mai hawa uku ya faɗo a kasuwar sayar da wayoyi ta Beirut da ke birnin Kano, wanda ya jawo asarar rayuka.

Sakataren hukumar agajin gaggawa ta LASEMA, Dr Olufemi Damilola Oke-Osanyintolu, ya ce an gano gawar mutum biyu kuma an fito da su.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da aikin zaƙulo sauran mutum huɗun da ake zaton ginin ya danne.

Leave a Reply