An Yi Gobara A Wani Sashen Gidan Sheikh Gumi A Kaduna

1
295

Daga; IMRANA ABDULLAHI, Kaduna.

AN samu tashin Gobara a wani bangare na gidan sanannen Malamin addinin Islama, Shaikh Ahmad Abubakar Gumi, a cikin garin Kaduna.

Ya zuwa yanzu dai bayanan da muke samu na musabbabin tashin Gobarar ba wasu masu karfi bane, domin bayannan da muke samu a halin yanzu daga wani da ya nemi a boye sunansa na cewa Gobarar ta tashi ne daga bangaren makarantar Islamiyya da ke gidan.

“Kawai mun dai ga hayaki ne ya na fitowa daga daya daga gillansan makarantar. Nan da nan kawai muka kawo hankalin mutane da ke wurin sai kawai muka fara nemo ruwa domin kashe wutar domin kada ta kama dayan bangaren”, inji majiyar.

Zamu kawo maku karin bayanin da ya samu nan gaba

1 COMMENT

Leave a Reply