An yi garkuwa da ɗan kasuwa, an harbe mutane biyu a kano

0
372

Daga Shafa’atu Dauda, Kano

Wasu masu garkuwa da mutane domin neman kuɗin fansa sun yi awon gaba da wani ɗan kasuwa mai suna Alhaji Nasiru Na’ayya mazaunin ƙauyen Gangarbi da ke ƙaramar hukumar Rogo a jihar Kano.

Wani ɗan’uwan wanda aka yi garkuwar da shi ɗin, wanda ya buƙaci a sakaye sunansa ya shaida wa jaridar Neptune prime cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 12 na ranar Litinin.

Ya ƙara da cewa bayan sun yiwa gidan ɗan kasuwar tsinke ne sai suka fara harbi kan mai uwa wabi, inda hakan ne ya jawo hankalin maƙwabta da sauran jama’ar ƙauyen.

KU KUMA KARANTA: Ban san yin garkuwa da mutane don karɓar kuɗin fansa laifi ba ne – Wanda ake zargi

“A lokacin da maƙwabta da al’ummar gari suka yi yunƙurin hana tafiya da ɗan kasuwar, ‘yan bindigar sun buɗe musu wuta, inda nan take suka hallaka mutum ɗaya, yayin da ɗayan ya ke kwance a Asibiti yana karɓar magani”

Wasu rahotanni dai sun bayyana cewa ƙauyen Gangarbi da sauran ƙauyukan da suka haɗa da Bari da Gwangwan na fuskantar barazanar masu garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.

A lokacin haɗa wannan rahoton wakiliyar Neptune prime ta tuntuɓi kakakin rundunar ‘yan Sandan Najeriya reshen jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa kan batun sai dai ya ce kawo yanzu ba su da labarin faruwar hakan.

Ana dai ci gaba da samun matsalar garkuwa da mutane a Najeriya musamman jihohin Arewa maso yamma da kuma tsakiyar Najeriya.

Duk da cewa ba a cika samun rahotannin garkuwa da mutane a jihar Kano ba kamar takwarorinta na sauran yankin, masana tsaro na ganin cewa idan ba a yi maganin abin ba bayan lokaci kaɗan wannan matsala kan iya mamaye ko ina.

Leave a Reply