An yanke wa akanta janaral ɗaurin shekara 21 kan kuɗin ‘yan fansho

0
417

An samu wani tsohon akanta a ofishin shugaban ma’aikata na Najeriya, Garba Abdullahi Tahir da laifin wawushe kuɗin ‘yan fansho da ya kai Naira miliyan 26 inda kuma aka yanke masa hukuncin shekara 21 a gidan yari.

Hukumar EFCC mai yaƙi da yi wa tattalin arziki zagon ƙasa ta Najeriya ce ta gurfanar da Garba Abdullahi gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja kan wasu laifuka bakwai da ke da alaƙa da almundahana.

KU KUMA KARANTA: An kai wa jami’an hukumar EFCC hari a Abuja da Imo

Da yake yanke hukunci, alƙalin kotun Inyang Ekwo ya ce EFCC ta tabbatar da tuhumar da take yi wa tsohon akantan inda kuma aka same shi da laifin aikata duka laifukan.

Mai shari’ar ya yanke masa hukuncin ɗaurin shekara uku-uku a kan dukkanin laifukan bakwai, jumulla ke nan zai shafe shekara bakwai a gidan maza.Wata sanarwa da kakakin hukumar EFCC, Wilson Uwajaren ya fitar ta ce tun farko wanda ake tuhumar ya musanta aikata laifukan da aka tuhume shi da su.

Leave a Reply