An tsare ɓarayi 2 kan satar buhun zoɓo 10 a Jigawa

0
83

Jami’an Hukumar Sibil Difens a Jihar Jigawa, sun cafke wasu mutum biyu da ake zargi da satar buhun zoɓo guda 10 a jihar.

Kakakin rundunar, ASC Badruddeen Tijjani Mahmud, ya ce an kama waɗanda ake zargin ne a ƙaramar hukumar Hadeja.

Ya ce, an kama su ne a ranar Lahadi 21 ga watan Janairu, 2024 da misalin ƙarfe 8:30 na safe a unguwar Gawuna da ke Hadeja.

A cewarsa an cafke su ɗauke da buhu 10 na zoɓo wanda ake zargin na sata ne.

KU KUMA KARANTA: An kama wasu manyan ɓarayin wayar salula da POS guda huɗu

Mahmud, ya ce bincikensu ya nuna cewa waɗanda ake zargin sun haɗa baki tare da fasa shagon wani Alhaji Yusuf Idris da ke Gawuna a ƙaramar hukumar Hadeja.

Ya ce sun yi awon gaba da buhu 10 na zoɓo.

Amma kakakin ya ce, an ƙwato buhun zoɓon gaba ɗaya, wanda darajarsa ta kai baira N362,250.

Kazalika, ya ce an kama ɓarayin da wasu ƙarafa da adduna da suke amfani da su wajen fasa shagunan al’umma a yankin.

Leave a Reply