An tafka muhawarar farko tsakanin shugaba Biden da Trump

0
59
An tafka muhawarar farko tsakanin shugaba Biden da Trump

An tafka muhawarar farko tsakanin shugaba Biden da Trump

Shugaban Amurka Joe Biden da tsohon shugaban ƙasar Donald Trump sun gwabza muhawara a daren Alhamis, inda suka fafata kan tattalin arziƙin Amurka da harkokin ƙasashen waje da haƙƙin zubar da ciki da kuma batun ƙaura daga kan iyakar Mexico zuwa Amurka.

“Muna tamkar a wata matalauciyar ƙasa a duniya kuma abin kunya ne,” in ji Trump ya faɗa yayin muhawarar da aka watsa ta talabijin ga ƙasa baki ɗaya, daga hedkwatar gidan talabijin na CNN da ke Atlanta.

“Ba a mutunta mu,” in ji Trump, yana zargin Biden. “Suna tunanin mu wawaye ne.”

Biden ya mayar da martani lokaci guda, yana kallon Trump. Tare da cewa “Wannan shi ne shugaban ƙasa mafi muni a tarihin Amurka. Wannan mutumin bai san ma’anar dimokuraɗiyyar Amurka ba.”

Haɗuwar Biden-Trump, watanni huɗu gabanin zaɓen ranar 5 ga watan Nuwamba, ita ce muhawara ta farko da aka taɓa yi a zagaye na huɗu na zaɓen shugaban ƙasar Amurka.

Hakanan sake haɗuwa ne tun muhawarar su guda biyu a shekarar 2020, wanda ya faru a cikin watanni biyu kafin Biden ya kayar da yunƙurin sake zaben Trump na wa’adi na biyu a Fadar White House.

Muhawarar ta ranar Alhamis ita ce karo na farko da shugabannin Amurka biyu suka taɓa yin muhawara a tsakaninsu, kuma shi ne karo na farko, da Biden da Trump suka haɗu a ɗaki ɗaya tun bayan muhawarar da suka yi a watan Oktoban 2020.

KU KUMA KARANTA:Biden ya yi alƙawarin kare Isra’ila daga harin ramuwar gayya na Iran

Trump ya tsallake bikin rantsar da Biden a watan Janairun 2021, kuma tun daga lokacin suka yi ta zage-zage da juna, ciki har da matakin muhawara a daren Alhamis.

A cikin ‘yan kwanakin nan, Trump ya yi ba a game da shirye-shiryen muhawarar Biden, inda ya ba da shawarar cewa zai bukaci ƙarin ƙarfi daga likita don samun damar iya muhawarar ta mintuna 90, gaba da gaba.

Trump ya faɗa wa wani gangamin magoya baya a Philadelphia cewa, “A yanzu haka, Joe ya tafi gidan katako don yin nazari,” yayin da yake zayyana alamomi da hannunsa. “Yanzu yana barci, saboda suna son ya samu ƙarfi.”

Leave a Reply