Daga; USMAN NASIDI, Kaduna.
A SAFIYAR ranar talata 22 ga watan Maris ne wani mummunar abun al’ajabi faru inda wani ibtila’i ya afkawa wani Editan Shafin Siyasa na gidan Jaridar New Nigerian Newspapers (NNN), Mista Amos Mathew yayin da aka sace masa mota kirar Golf 3; Samfurin Ba’amurke mai lamba LSD-516-HB, a sakatariyar Jam’iyyar APC dake Kaduna.
Ana zargin wasu ‘yan bangar siyasa ne suka sace motar mai launin bakar fata.
Motar da aka sace an ajiye ta ne a gaban Sakatariyar jam’iyyar APC inda aka gayyaci ‘yan jaridu domin daukar rahotannin bayanin wani Dan takarar gwamna na Jam’iyyar APC.
Sai dai ‘yan jaridu a Jihar, sun yi Allah wadai da wannan mummunar al’amarin, kana da yin barazanar kauracewa duk wasu harkokin siyasa a Jihar nan gaba, idan hukumomin da abin ya shafa suka kasa daukar matakin gano motar.
A cewar Mista Mathew, ya ajiye motar ne a gaban Sakatariyar Jam’iyyar da misalin karfe 10:00 na safe, kuma an gano ba motar ne a karshen taron yan siyasar bayan da wasu ‘yan bangar siyasar da ba a san ko su waye ba suka sace ta da misalin karfe 11:20 na safiyar ranar Talata.
Ya bayyana cewa an sanar da hukumar ‘yan sanda da sauran hukumomin da abin ya shafa kan wannan mummunar al’amarin daya auku.
Acewarsa, da akwai wasu kayayyaki masu daraja kamar: katin ATM, katin shaida na ofis, katin zabe, katin shaida na dan kasa da dai sauransu na cikin motar da aka sace.