An rasa yara 2 da gidaje sama da dubu ɗaya a gobarar sansanin gudun hijira a Borno

0
201

Ƙananan yara biyu sun rasu gidaje 1,113 sun ƙone a sakamakon gobarar da ta tashi a ranar Laraba a sansanin ’yan gudun hijira da ke yankin Muna Alamdari a ƙaramar hukumar Mafa ta jihar Borno.

Gobarar ta ranar Laraba ta tashi ne a yayin da ake cikin jimamin wadda ta tashi a a ƙarshen mako a Babbar kasuwar Gamborou da ke Maiduguri babban birnin jihar.

Kodinetan Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno a Karamar Hukumar Mafa, Surajo Garba, ya ce yara maza ’yan shekaru bakwai da 10 ne suka rasu a gobarar.

“Gidaje 1,113 sun kone, wasu 50 kuma an yi amfani da su wajen aikin agajin gaggawa,” in ji Surajo.

Ya ci gaba da cewa ba a kai ga gano musabbabin tashin gobarar ba tukuna, haka kuma ba a tantance yawan dabbobi da sauran ƙadarorin da gobarar ta lalata ba.

A jawabinsa bayan ziyarar gani da ido da ya kai sansanin ’yan gudun hijirar da aka samu gobarar, Darakta-Janar na hukumar, Barkindo Muhammad, ya ce wutar ta tashi ne da misalin karfe 6 na safe, sai bayan awanni ’yan kwana-kwana da taimakon sauran hukumomi da jama’ar gari suka shawo kanta.

KU KUMA KARANTA: Gobara ta tashi a kasuwar Gamboru da ke Maiduguri

“Muna jajantawa kuma za mu ba da tallafin gaggawa da suka haɗa da buhu 500 na shinkafa, da barguna da sauran kayayyaki nan take,” in ji shi.

Karo na biyu ke nan da aka samu tashin gobara a sansanin, bayan makamancinsa a watan Fabrairum wanda ya ƙone bukkoki 200.

Wancan lokaci hukumomi sun gobarar ta tashi ne da misalin karfe 11 na safe bayan yawancin mazauna sansanin sun shiga gonaki neman abninci.

Akasarin waɗanda abin ya shafa, babu abin da suka tsira da shi sai kayan jikinsu.

A watan Nuwamban 2022 an samu gobara a sansanin ’yan gudun hijirar da ke Ƙaramar Hukumar Mafa, mako uku bayan tashin watto gobarar a sansanin ’yan gudun hijira a Ƙaramar Hukumar Konduga da kuma wata gobarar a Maiduguri.

A watan Fabrairun 2022, wasu gidaje 100 suka ƙone a sansanin ’yan gudun hijira na Muna El-Badawi da ke Maiduguri a sakamakon fashewar tukunyar iskar gas.

A shekarun da suka wuce ne Hukumar Raya yankin Arewa maso Gabas (NEDC), da ƙungiyoyin agaji da attajirai suka gina dubban gidaje domin sake tsugunar da ’yan gudun hijira, ko da yake har yanzu wasu dubbai na zaman jiran tsammani a matsugunan wucin gadi da aka samar musu.

Leave a Reply