An Kammala Shirye-Shiryen Taron Sulhu Na APC Gobe – Ganduje

0
319

Daga; Jabiru Hassan, Kano.

SHUGABAN kwamitin hadin gwiwa na Jam’iyyar APC na kasa da jiha, kuma gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa kwamitin ya kammala shirye-shiryen karbar sauran mambobin kwamitin domin gudanar da taron sasantawa a Jihar.

Wata sanarwa da kwamishinan yada labarai na Jihar, Malam Muhammad Garba ya fitar, ta ruwaito gwamnan na cewa an tanadi wurin da za a gudanar da taron da aka shirya Wanda za a fara ranar Juma’ar nan watau 11 ga watan Fabrairu, 2022 a babban birnin Jihar.

Gwamna Ganduje ya tabbatar wa ‘ya’yan sakatariyar Jam’iyyar APC ta kasa da masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar a Jihar cewa a shirye kwamitin ya ke na bayar da tawaga ga duk wanda ya damu da shi da nufin kawo hadin kai da ci gaba a Jam’iyyar a Jihar da kasa baki daya.

Kwamitin wanda Sakatariyar Jam’iyyar ta kasa ta kafa, yana kunshe da wasu mambobi ksmar Sardaunan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau, Gwamna Bello Matawalle, Hon. Yakubu Dogara da Sanata Abba Ali, sannan Kwamitin na da kwanaki bakwai domin mika rahotonsa.

Leave a Reply